'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Janye Saura Awanni a Fita Zaɓe? Gaskiya Ta Bayyana
- Ɗan takarar Gwamnan jihar Imo a inuwar jam'iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya musanta rahoton janyewa daga tseren takara
- Ya musanta faifan bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya a wata sanarwa da kwamitin yaƙin neman zaɓen SamJone ya fitar ranar Jumu'a
- Ya yi kira ga mutanen jihar Imo da su yi watsi da bayanan cikin bidiyon domin ƙarya ce da aka kirkira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Imo - Kwamitin kamfen SamJones ya musanta faifan bidiyon da ke yawo a soshiyal mediya cewa ɗan takarar Gwamna a inuwar PDP, Samuel Nnaemeka Anyanwu, ya janye daga zaben jihar Imo.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kwamitin yaƙin neman zaben ya bayyana labarin da ƙarya, yana mai cewa babu wani abu mai kama da haka da ya faru.
Kwamitin kamfen PDP ya musanta rahoton
Wannan ƙarin haske na ƙunshe ne a wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaben SamJones, Dumebi Ifeanyichukwu, ya fitar ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi kira ga ɗaukacin al'ummar jihar Imo su yi watsi da irin waɗannan rahoton domin ba su da tushe, ɗan takarar PDP na nan daram a cikin ƴan takara.
A rahoton Punch, sanarwan ta ce:
"Ya zama tilas Kwamitin kamfen SamJones ya yi magana kan wani mugun faifan bidiyo da ke yawo, ɗauke da karyar cewa mai girma dan takararmu, Sanata Samuel Nnaemeka Anyanwu, ya janye daga takarar gwamnan Imo."
"Muna sanar da al'umma cewa rahoton karya ce. Bayan nazarin faifan bidiyon, ya bayyana cewa an yi masa gyara sosai da sautin murya domin a yaudari jama'a."
"Muna kira ga ɗaukacin al'umma da su yi watsi da abinda ke cikin faifan bidiyon gaba ɗaya."
Sanata Anyanwu na daya daga cikin ‘yan takarar da ke kan gaba a zaben. Yana adawa da gwamna mai ci, Hope Uzodimma, na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Matawalle ya soki Gwamnatin Buhari
A wani rahoton kuma Matawalle ya bayyana cewa tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ba ta ɗauki batun tsaro da muhimmancin da ya kamata ba.
Ƙaramin Ministan tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya ce ma'aikatar su ta kawo sabbin jiragen yaƙin domin kawo karshen.lamarin.
Asali: Legit.ng