Kamfen PDP: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Arewa Kan Muhimmin Abu, Hotuna Sun Bayyana
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya dira jihar Kogi domin goyon bayan Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP
- A wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa mai kunshe da Hotuna, an ga manyan jiga-jigan tare da juna
- Alhaji Atiku ya tabbatar da cewa shi da tawagarsa sun ziyarci Kogi ne domin halartar gangamin kamfe da goyon bayan Melaye
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ƙara nuna goyon bayansa ga Sanata Dino Melaye a zaben jihar Kogi.
Sanata Melaye, shi ne ɗan takarar Gwamnan jihar a zaben da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 karƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
Atiku ya tabbatar da cewa tuni ya dira jihar Kogi domin halartar gangamin yaƙin neman zaben jam'iyyar PDP gabanin zaɓen na ranar Asabar mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Tuwita mai kunshe da Hotuna.
A rubutun da ya wallafa ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, 2023, Atiku ya ce:
"Yanzu haka tawagata da ta jam'iyyar PDP na gidan Sanata Tunde Ogbeha domin halartar ralin Sanata Dino Melaye, ɗan takarar Gwamna a inuwar PDP a zaben ranar Asabar."
A hotunan da Legit Hausa ta ci karo da su, an ga Sanata Melaye tare da Atiku Abubakar, muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagun da mataimakiyar Melaye, Habeebat Deen.
Melaye zai fafata da manyan ƴan takara 2
Sanata Melaye zai gwabza da ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar APC, Alhaji Usman Ododo, wanda ke da goyon bayan Gwamna mai ci, Yahaya Bello.
Haka nan kuma zai fafata da ɗan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka, wanda ya fito daga ƙabilar Igala, wacce ta fi girma da yawan al'umma a jihar Kogi.
Fasto Uno ya ƙara wa ma'aikata albashin wata ɗaya
A wani rahoton na daban Gwamna jihar Akwa Ibom ya amince da biyan ma'aikatan jiharsa albashin watan 13 domin su yi shagalin kirsimeti.
Fasto Umo Eno, ya ba da umarnin biyan kowane ma'aikaci kwatan-kwacin albashinsa a matsayin tallafin bikin kirsimetin 2023.
Asali: Legit.ng