Murna Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Mayar da Dan Majalisar PDP a Jihar Arewa Kujerarshi, Ya Gode

Murna Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Mayar da Dan Majalisar PDP a Jihar Arewa Kujerarshi, Ya Gode

  • Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin Abuja ta yanke hukunci kan shari'ar zaben majalisar jihar Taraba
  • Kotun ta mayar wa Honarabul Nuhu Akila na jam'iyyar PDP kujerarshi a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Lau
  • Har ila yau, kotun ta rusa hukuncin kotun zabe da ta bai wa Emmanuel George na jam'iyyar PDP nasara yayin hukuncinta

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara ta mayar da dan majalisar jihar Taraba, Honarabul Nuhu Akila na jam'iyyar PDP kujerarshi.

Kotun ta yanke hukuncin a yau Alhamis a birnin Tarayya Abuja bayan daukaka kara da ya yi na kalubalantar hukuncin kotun zabe.

Kotu ta mayar wa dan takarar Majalisar jihar Taraba kujerarshi
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Majalisar jihar Taraba. Hoto: Court of Appeal.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta gama aiki, ta yanke hukunci kan nasarar dan majalisar tarayya na PDP

Akila wanda dan jam'iyyar PDP ne na wakiltar mazabar Lau a majalisar jihar inda ya yi nasara kan dan jam'iyyar APC, Emmanuel George a zaben majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun zabe a yayin hukuncinta, ta kwace kujerar Akila inda ta bai wa George na jam'iyyar APC nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Kotun ta yi hukuncin bayan samun gamsassun hujjoji cewa George na APC ya fi samun kuri'u ma su yawa fiye da Akila a zaben, Latest News ta tattaro.

Wane mataki Akila ya dauka?

Daga bisani Nuhu Akila ya daukaka kara inda ya ke neman kotun ta dawo ma sa da kujerarshi da hukumar zabe ta mallakar ma sa, cewar The Nation.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Uche Onyemenan ya ce an tafka kura-kurai yayin hukuncin kotun zaben da ta rusa nasarar Akila.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Ministan Tinubu wanda ya lashe zaben sanata a jihar Arewa

Ya ce dukkan shaidun da su ka gabatar ba su da tushe yayin da wasu daga cikinsu jita-jita ce kawai babu kamshin gaskiya.

Kotu daukaka kara ta tabbatar da nasarar Kingibe

A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da Sanata Ireti Kingibe a matsayin wacce ta lashe zaben sanatar Abuja.

Kingibe wacce 'yar jam'iyyar LP ce ta yi nasara kan dan takarar jam'iyyar PDP, Philip Tanimu Aduda a zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.