Akpabio Ya Tura Muhimmin Sako Ga Tinubu Kan Ma Su Kin Bin Umarnin Majalisar, Ya Fadi Dalili

Akpabio Ya Tura Muhimmin Sako Ga Tinubu Kan Ma Su Kin Bin Umarnin Majalisar, Ya Fadi Dalili

  • Godswill Akpabio, shugaban Majalisar Dattawa ya yi gargadi ga ma su rike da mukamai da ke kin amsa gayyatar Majalisar
  • Akpabio ya kirayi Tinubu da ya dauki mataki kan irin wadannan ma su mukamai da ke kin bin umarnin Majalisar
  • Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba yayin wani babban taro a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bukaci Shugaba Tinubu ya kori ma su mukamai da ke bijirewa umarnin Majalisar.

Akpabio na magana ne kan ma su rike da madafun iko da ke kin amsa gayyatar Majalisar don karin bayani ko wani abu makamancin haka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake nada shirgegen mukami mai muhimmanci a gwamnatinsa, an fadi sunan matashin

Akpabio ya bai wa Tinubu shawara kan korar ma su kin bin umarnin Majalisar
Akpabio ya tura sako ga Tinubu. Hoto: Godswill Akpabio, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Akpabio ya ce wa Tinubu?

Shugaban Majalisar ya bayyana haka a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba yayin wani taro a dakin Majalisar da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin kudade na Majalisar ne ya hada wannan taro don nemo hanyoyin kara kudaden shigar Gwamnatin Tarayya, Daily Trust ta tattaro.

Akpabio ya ce wannan taro ya na da matukar muhimmanci ga dukkan wani mai mukami da ke son ci gaban gwamnatin Tinubu.

Ya ce dole ko wa ne mai mukami a wannan Gwamnati ya halarci wannan taro musamman mai son ci gaban gwamnatin Tinubu, cewar Tribune.

Wani sako Akpabio ya tura wa Tinubu?

Ya kara da cewa saboda mihimmancin wannan taro haka ya bar kamfen yakin neman zaben jam’iyyar APC a Owerri a jihar Imo, cewar Punch.

Ya ce:

“Duk wani wanda ya dauki mukaminsa da muhimmanci da ya ke son ci gaban gwamnatin Tinubu ya kamata ya na nan wurin.

Kara karanta wannan

Satar mazakuta: tsagera sun yi wa lakcara dukan kawo wuka a jihar Arewa, 'yan sanda sun fusata

“Shugaba ka ba ni dukkan sunayen wadanda ka gayyata da su ka ki zuwa nan wurin don halartar wannan taron.”

Ya kara da cewa duk wani mai mukami da ya tura wakili bai dauki mukamin da muhimmanci ba, ya kamata Tinubu ya sake tunani a kan shi.

Akpabio ya ce wannan abin da ya ke fada ba barazana ba ce illa tsagwaron gaskiya wanda ta na da daci.

Akpabio ya gargadi shugaban EFCC

A wani labarin, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi sabon shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode.

Akpabio ya umarci Ola da ya bar misali da sunansa yayin tantance shugaban hukumar ta EFCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.