“Ni Matar Aure Ce”: Ododo, Dan Takarar APC a Kogi Ya Yi Barambarama Yayin da Ya ke Shagube Ga Dino

“Ni Matar Aure Ce”: Ododo, Dan Takarar APC a Kogi Ya Yi Barambarama Yayin da Ya ke Shagube Ga Dino

  • An gano dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kogi, Usman Ododo, yana kiran kansa da mace
  • Ga dukkan alamu Ododo na yin shagube da abokin adawarsa na PDP, Dino Melaye ne wanda bai da aure
  • Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na bidiyon don yin martani daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

An gano Usman Ododo, dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben ranar Asabar da za a yi a jihar Kogi a cikin wani bidiyo yana yin barambarama yayin da yake jawabi ga taron jama’a inda ya kira kansa da “matar aure”.

Ana zargin cewa dan takarar gwamnan na APC yana kokarin yin shagube ne ga babban abokinb hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Dino Melaye, wanda bai da aure.

Usman Ododo ya yi shagube ga Dino Melaye
“Ni Matar Aure Ce”: Ododo, Dan Takarar APC a Kogi Ya Yi Barambama Yayin da Yake Shagube Ga Dino Hoto: Usman Ododo, Dino Melaye
Asali: Twitter

Usman Ododo na APC ya yi barambarama

A dan gajeren bidiyon, an jiyo Ododo yana cewa:

Kara karanta wannan

Fitaccen dan takarar gwamnan jihar Kogi ya janye ana dab da zabe? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna so mu baku tabbacin cewa Ni, Ahmed Usman Ododo, ni matar aure ce, ina da kamun kai."

Wani mai suna Morris Monyo ne ya wallafa bidiyon dan takarar na APC a Twitter a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.

"Kalli mai kwakkwalwar da APC take da shi da za ta bayar a jihar Kogi a matsayin Gwamna."

Ga wallafar a kasa:

Yadda yan Najeriya suka yi martani ga barambaramar Ododo

Da suke martani a sashin sharhi, wasu yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu. Duba martaninsu a kasa:

Joseph Arinze ya roki Allah ya kawowa Najeriya dauki daga hannun APC. Ya ce:

"Allah, shin za ka ceto Najeriya daga hannun APC?"

Maestro ya nuna yakinin cewa mutanen jihar ba za su yi wani abu a kai ba. Ya ce:

"Mutanen Kogi na kallo kuma abun bakin ciki ba lallai su yi wani abu a kai ba."

Kara karanta wannan

Kwadayi Ya Jawo Mana: Jagora a PDP Ya Fadi Wadanda Su ka Yi Sanadiyyar Fadi Zabe

Ifeanyichukwu ya bukaci APC da ta yi waje da mambobin da basu cancanta ba. Ya ce:

"APC ta yi waje da baragurbin mambobinta idan har tana so ta rayu bayan Tinubu."

Malami ya hango bala'i a zaben Kogi

A wani labarin kuma, mun ji cewa Fasto Eneojo Suleman, ya hango gagarumin bala'i tattare da zaben gwamna a jihar Kogi.

Fasto Suleman wanda yake haifaffen jihar ya ce za a yi rikici sosai a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng