Kotun Daukaka Kara Ta Gama Aiki, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Dan Majalisar Tarayya Na PDP
- Dan majalisar wakilai na jihar Imo ya samu nasara a kotun daukaka kara, reshen jihar Lagas
- A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, kotun daukaka karar ta tabbatar da zaben Hon. Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu
- Bayan hukuncin kotun, doguwar shari'ar da aka yi da dan majalisar na PDP ta zo karshe
Jihar Lagos - Bayan doguwar shari'a da aka dade ana yi, kotun daukaka kara, reshen lagas, ta tabbatar da zaben Hon. Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Ideato ta arewa da kudu ta jihar Imo a majalisar wakilai.
Dan majalisa na jihar Imo ya yi nasara a kotun daukaka kara
Da take yanke hukunci a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, kotun ta ayyana Hon. Ikenga Ugochinyere a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai a jihar Imo a zaben na watan Fabrairu.
Daily Trust ta rahoto cewa karar da ta shafi zaben majalisar dokokin tarayya ta kare a kotun daukaka kara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hukuncin da ya yanke, kwamitin kotun karkashin jagorancin mai shari’a Abubakar Babandi Gumel ya kuma yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Imo ta yanke.
Da yake magana bayan hukuncin kotun daukaka karar, lauyan Ikenga Imo Ugochinyere, Emeka Ozoani, SAN, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga damokradiyya da kawo karshen son kai a siyasance, rahoton Leadership.
Kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 3
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja, a hukuncin da ta yanke lokuta daban-daban ranar Talata, ta tabbatar da tsige ƴan majalisar wakilan tarayya uku daga jihar Filato.
Dukkan ƴan majalisun uku da suka rasa kujerunsu sun samu nasara ne ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Kotun ta amince da korar su daga majalisar wakilan tarayya bisa rashin halascin takarar da suka tsaya karƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
Waɗanda Kotun ɗaukaka ƙara ta yi na'am da tsige su sun haɗa da, Peter Gyendeng mai wakiltar mazaɓar Barkin-Ladi/Riyom a majalisar wakilan tarayya.
Asali: Legit.ng