Ana Saura Kwanaki 3 Zaben Gwamna, a Karshe Tsohon Shugaban Kasa Ya Bayyana Wanda Ya Ke Muradi
- Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ya bayyana ra’ayinsa kan dan takarar da ya kamata mutane su zaba a Bayelsa
- Jonathan ya bayyana matsayarsa inda ya marawa Gwamna Douye Diri baya a zaben da za a gudanar a wannan wata
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatarensa a bangaren yada labarai, Daniel Alabrah ya fitar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa – Tsohon shugaba kasa, Dakta Goodluck Jonathan ya bayyana dan takarar da ya ke so a zaben gwamnan jihar Bayelsa.
Jonathan ya bayyana haka ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a ranar 11 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.
Waye Jonathan a goya wa baya a Bayelsa?
Tsohon shugaban kasar ya ce ya na tare da Gwamna Douye Diri na jam’iyyar PDP don samun damar wa’adi na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Diri ne ya dace da kujerar ganin yadda ya daidaita jihar tare da kawo abubuwan ci gaba da kuma tsaro.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatarensa a bangaren yada labarai, Daniel Alabrah ya fitar a jiya Talata 7 ga watan Nuwamba.
Mene Jonathan ke cewa kan zaben Bayelsa?
Sanarwar ta ce:
“Ina yawan magana da gwamanmu, ina ga ya dace a mara ma sa baya don samun wa’adi na biyu saboda kawo sauyi a wannan jiha.
“Ya kamata mu samu hanyar aiwatar da abubuwa, ba ma son tashin hankali, mun gode da abubuwan da ka ke yi.
“Yayin da mu ke ci gaba da buga-bugar neman shugabanci, dole mu samu kasa wacce za mu yi alfahari da ita.”
Vanguard ta tattaro cewa Jonathan ya bayyana haka yayin da mambobin jam’iyyar PDP a jihar da tsoffin gwamnonin PDP su ka kai ma sa ziyara a Yenagoa.
Jiga-jigan jam’iyyar sun kai ziyarar jihar Bayelsa don halartar kamfe na karshe na Gwamna Diri da ke neman zarcewa a zaben.
Gwamna Diri ya shiga matsala
A wani labarin, ana saura kwanaki kadan a gudanar da zaben jihar Bayelsa, Gwamna Diri ya shiga gagarumar matsala.
Wata mata da maka Gwamna Douye Diri da mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo a babbar kotun Tarayya da ke Abuja.
Asali: Legit.ng