Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Yanke Hukunci Kan Zaben Majalisar Tarayya, Ta Yi Bayani
- Kotun daukaka kara a yau Litinin ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Kano
- Kotun ta tabbatar ma nasarar dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Yusuf Takai a matsayin wanda ya lashe zabe
- Hassan Sani Tukur, hadimin gwamnan Kano a bangaren yada labarai na zamani shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a yau Litinin
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar da ake a mazabar Tarayya ta Takai/Sumaila a jihar Kano.
Kotun wacce ta yanke hukunci a yau Litinin 6 ga watan Nuwamba ta tabbatar da nasarar Rabiu Yusuf Takai na jam'iyyar NNPP.
Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?
Hadimin Gwamna Abba Kabir na Kano a bangaren yada labarai ta zamani, Hassan Sani Tukur shi ya bayyana haka a shafin Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin fara sauraran shari'ar zaben gwamnan jihar Kano tsakanin Abba Kabir da Nasiru Gawuna.
Yayin hukuncin kotun zabe a watan Satumba, kotun ta tabbatar da Yusuf Takai a matsayin dan Majalisar Tarayya, tare da tarar naira dubu 20.
Hukunci a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam
Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam.
Yayin hukuncin, kotun ta rusa zaben Musa Ilyasu Kwankwaso na jam'iyyar APC.
Ta kuma tabbatar da Yusuf Datti na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zabe.
Hukuncin na zuwa bayan korafe-korafen da dan takarar jam'iyyar NNPP, Datti ya shigar a gaban kotun bayan hukuncin kotun kararrakin zabe.
Kotu ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti a jihar Kano
A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya da ke jihar Kano.
Kotun ta rusa nasarar Musa Ilyasu Kwankwaso na jam'iyyar APC a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam da ke jihar.
Har ila yau, kotun ta tabbatar da Yusuf Datti na jam'iyyar NNPP a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben Majalisar Tarayya.
Asali: Legit.ng