Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Dan Majalisar Tarayya, Ta Fadi Mai Nasara

Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Dan Majalisar Tarayya, Ta Fadi Mai Nasara

  • A yau Litinin, 6 ga watan Nuwamba kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Kano
  • Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar NNPP, Yusuf Datti a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Hassan Sani Tukur, hadimin gwamnan Kano a bangaren yada labarai na zamani shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar da ake a mazabar Tarayya ta Kura/Madobi/Garun Malam a jihar Kano.

Kotun wacce ta yanke hukunci a yau Litinin 6 ga watan Nuwamba ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti na jam'iyyar NNPP, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Ministan Tinubu wanda ya lashe zaben sanata a jihar Arewa

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti a jihar Kano
Kotun daukaka kara ta yi hukunci a zaben Majalisar Tarayya a Kano. Kwankwasiyya/ Facebook.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun daukaka ta yanke a Kano?

Hadimin Gwamna Abba Kabir na jihar Kano a bangaren yada labarai ta zamani, Hassan Sani Tukur shi ya bayyana haka a shafin Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin fara sauraran shari'ar zaben gwamnan jihar Kano tsakanin Abba Kabir da Nasiru Gawuna.

A baya, kotun zabe ta rusa zaben Gwamna Abba Kabir na NNPP tare da tabbatar da Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zabe.

Mene kotun ta ce kan karar APC?

Kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso da rashin hujjoji.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Tunde Awotoye ya tabbatar da cewa kotun zaben yayin hukuncinta ta yi kuskure.

Ta ce kotun ba ta da hurumin yin hukunci kan kasancewar shi mamba a jam'iyyar musamman kan hukuncinsu na murabus a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: Abubuwa 12 da Kotun Daukaka Kara Za Ta Duba a Shari'ar Zaben gwamnan Kano

Kotu ta yi hukunci kan zaben Majalisar Tarayya a Kano

A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar da ake yi na zaben Majalisar Tarayya a jihar Kano.

Kotun ta tabbatar da Rabi'u Yusuf Takai a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar Tarayya a jihar.

Kotun ya yi hukuncin ne a zaben da ka gudanar a watan Faburairu na farko wannan shekara da mu ke ciki a mazabar Takai/Sumaila da ke jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.