Zaben Kogi: Al'ummar Fulani Sun Bayyyana Dan Takarar da Su Ke Goyon Baya

Zaben Kogi: Al'ummar Fulani Sun Bayyyana Dan Takarar da Su Ke Goyon Baya

  • Ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya samu tagomashi
  • Al'ummar Fulani na jihar sun nuna goyon bayansu a gare shi a zaɓen gwamnan na ranar 11, ga watan Nuwamban
  • Al'ummar Fulanin sun bayyana cewa sun gamsu da cancantar Ododo domin jagorantar jihar Kogi

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kogi - Al’ummar Fulani a jihar Kogi sun nuna goyon bayansu ga ɗan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Ahmed Ododo gabanin zaɓen gwamnan jihar ranar Asabar mai zuwa.

Mai magana da yawun al'ummar Fulani, Farfesa Mohammed Abdullahi wanda ya yi magana a madadin al'ummar ya ce an zaɓi Ododo ne saboda ya fi cancanta a cikin ƴan takarar da ke neman kujerar gwamnan.

Kara karanta wannan

Yaudara ko don Allah? Yahaya Bello ya ware miliyan 497 don dalibai ana saura kwanaki 6 zabe a jihar

Fulani sun nuna goyon bayansu ga Ahmed Usman Ododo
Al'ummar Fulani a Kogi sun goyi bayan Ahmed Usman Ododo Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa sun cimma wannan matsayar ne duba da gagarumar nasarar da gwamnatin Gwamna Yahaya Bello ta samu, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa ga al'ummar jihar, rahoton Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Fulani ke goyon bayan Ododo?

A kalamansa:

"Mun san Ododo ne ya fi cancanta a cikin dukkanin ƴan takarar da ke neman kujerar gwamna."
"Mun tattauna da sauran ƴan takarar kuma mun gani cewa shi (Ahmed Ododo) ne ya fi cancanta a cikinsu."
"Na biyu, duk ayyukan da Yahaya Bello ya fara bai kamata su tsaya ba. Muna son Ododo ya cigaba da aikin Gwamna Bello na sake gina jihar Kogi."
"Gwamnatin Gwamna Bello ta yi mana karamci. Gwamnatinsa gwamnati ce mai ɗaukar nauyin kowa, ba tare da la’akari da kabilarku ko addininku ba kuma muna ganin Ododo yana bin sawunsa.”

Kara karanta wannan

Zaben Bayelsa: Gwamna Diri na Bayelsa ya shiga matsala ana dab da zabe

Ododo ya yi musu alƙawari

Da yake nasa jawabin, Ahmed Usman Ododo, ya buƙaci jama'a da su zabe shi ya ƙara da cewa yana da kyakkyawar niyya a kan jihar.

"Idan aka zaɓe ni, zan tabbatar da cewa kun sami yancin cigaba da gudanar da kasuwancin ku, kuma yaranku za su cigaba da zuwa makaranta ba tare da tsangwama ba." A cewarsa.
"Ina ƙara tabbatar muku da cewa idan aka zabe ni a matsayin gwamna, zan naɗa ɗan ƙabilar Fulani a cikin majalisar ministocina."

Abubuwan da Za Su Yi Tasiri a Zaben Kogi

A wani labarin kuma, mun tattaro muku abubuwan da za su yi tasiri a zaɓen gwamnan Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Zaɓen dai akwai manyan ƴan takara uku na jam'iyyun APC, PDP da SDP waɗanda za su fafata domin neman gaje kujerar Gwamna Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng