Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Tsohon Gwamnan Gombe
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje, ya tabbata kan kujerarsa a matsayin dan majalisa mai wakiltan yankin jihar ta tsakiya
- Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasararsa a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, bayan ta kori karar Abubakar Aliyu na PDP
- Kwamitin mutum uku na alkalan kotun sun yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar adawa saboda ya gaza gabatar da kwakkwarar hujja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar Danjuma Goje a matsayin sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya.
Kwamitin mutum uku na alkalan kotun sun yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar PDP, Abubakar Aliyu, dangane da zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, rahoton Daily Trust.
Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben majalisa a Gombe, wacce a baya ta kori karar da Aliyu da PDP suka shigar kan Goje da jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu karar, karkashin jagorancin lauyansu Edwin Okoro, sun yi zargin cewa an tafka magudi da rashin tsari a yayin zaben, lamarin da ya shafi Goje, APC, da kuma Hukumar zabe mai ta kasa mai zaman kanta (INEC), Politics Nigeria ta rahoto.
Amma alkalan kotun uku karkashin jagorancin Mai shari’a Biobele Georgewill, sun amince da hukuncin kotun zaben, tare da yin watsi da karar, saboda rashin samun hujjoji daga bangaren masu shigar da kara wanda zai nuna cewa Goje ya shiga zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP.
Kotu ta yi a zaben sanatan Kogi
A wani labarin, mun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da nasarar shugaban kwamitin kwastam na majalisar dattawa, Sanata Jibrin Isah.
Yayin zaman yanke hukunci ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, Kotun ta bayyana cewa shaidun da Kotun zaɓe ta dogara da su a shari'ar sam ba su inganta ba.
Sakamakon haka Kotun ɗaukaka karar ta yanke yin fatali da dukkan bayanan da shaidun suka yi a shari'ar sahihancin zaɓen Sanata Isah, mai wakiltar Kogi ta gabas.
Asali: Legit.ng