Kano: Kotun Koli Ta Yi Hukunci Kan Zaben Gwamna da Aka Kora a Kotun Jihar
- Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jihar Abia a zaben da aka gudanar a watan Maris
- Tun farko, kotun daukaka kara ta yi fatali da hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben a jihar Kano saboda rashin hujjoji
- Kotun kolin ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Ambrose Ahiwe saboda rashin gamsassun hujjoji da zai ruguza zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun koli ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Abia, Alex Otti da PDP ke kalubalanta.
Kotun daukaka kara a kwanakin baya ta yi fatali da hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe da ke zamanta a jihar Kano, Legit ta tattaro.
Wane hukunci kotun koli ta yanke kan Gwamna Otti?
Bayan hukuncin kotun zaben da ta rusa zaben Gwamna Otti, ya daukaka kara a kotu da ke jihar Kano inda ta yi watsi da hukuncin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar, Ambrose Ahiwe na kalubalantar zaben Otti wanda dan jam'iyyar LP ne a zaben.
Kotun kolin ta yi watsi da korafe-korafen Ahiwe inda ta ce kwata-kwata ba shi da hujjoji gamsassu a karar da ya ke yi.
Ahiwe ya daukaka kara a kotun koli
Har ila yau, kotun kolin bayan fatali da karar, ta ci tarar dan takarar jam'iyyar PDP, Ahiwe naira dubu 500.
Ahiwe dai ya daukaka kara bayan kotun daukaka kara ta kori hukuncin kotun zabe a jihar Kano, cewar BusinessDay.
Otti dai ya tsaya takarar gwamna a jam'iyyar LP a zaben da aka gudanar a watan Maris na farkon wannan shekara.
Kotun zabe ta kwace kujerar Abba Kabir a Kano
A wani labarin, Kotun zabe ta rusa zaben Gwamna Abba Kabir na Kano wanda jam'iyyar APC ke kalubalanta.
Kotun har ila yau, ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.
Tuni Gwamna Abba Kabir ya daukaka kara inda ya ce wannan hukunci tsantsar zalunci ne a ciki da kura-kurai yayin yanke shi.
Asali: Legit.ng