Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Zaben Dan Majalisar Tarayya a Kaduna
- Kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar zaben majalisar Tarayya a mazabar Jema'a/Sanga da ke jihar Kaduna
- Yayin hukuncin, kotun ta tabbatar da nasarar Daniel Amos na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben
- Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Mista Usman Anto saboda rashin gamsassun hujjoji
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar zaben majalisar Tarayya a jihar Kaduna.
Kotun ta tabbatar da Daniel Amos na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben a mazabar Jema'a/Sanga a majalisar Tarayya, Legit ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke kan shari'ar ta Kaduna?
Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Mista Usman Anto saboda rashin gamsassun hujjoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaben da aka gudanar a watan Faburairu, hukumar zabe ta INEC ta ayyana Daniel Amos a matsayin wanda ya lashe zaben, cewar NewsNow.
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a Samuel Ademola Bolaji ya ce Anto ya gaza kawo kwararan hujjoji na korafinsa a kan Daniel Amos.
Kotun ta soki tsarin da aka bi na rusa zaben a baya
Alkalan kotun sun soki kotun daukaka kara kan yanke hukunci ba tare da samun hujjoji gamsassu ba yayin hukuncin nasu.
Kotun ta bayyana cewa dukkan shaidun da kotun baya ta yi amfani da su ba su kai su rusa zaben Daniel Amos ba.
Ta yi fatali da karar inda ta ce babu wasu shaidu da za su tabbatar da gaskiyar abin da ake karar.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Ireti a Abuja
A wani labarin, Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Ireki Kingibe a matsayin wacce ta lashe zaben sanatar Abuja.
Kotun har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Philip Tanimu Aduda da ke kalubalantar zaben.
Aduda ya shafe shukaru da dama a kan wannan kujera ta sanata a mazabar birnin Tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng