Gwamnonin PDP Sun Yi Fatali da Tsagin Atiku, Sun Koma Bayan Shugaban Tinubu Kan Abu 1 Tak
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana dalilinsu na mara wa shugaban ƙasa Tinubu baya kan rikicin siyasar jihar Ribas
- A cewarsu, saɓanin tunanin masu sukar hakan wanda ke tare da Atiku, tsoma bakin Tinubu ya zama wajibi kuma dole a yaba masa
- Wannan na zuwa ne yayin da Ministan Abuja ya ce ba ruwansa da harkokin mulkin Ribas amma zai kare tsarin siyasar da aka kafa a 2015
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnonin jam'iyyar PDP sun jaddada goyon bayansu ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan yunkurinsa na shiga tsakani a rikicin siyasar jihar Ribas.
Sun bayyana cewa ƙungiyar gwamnonin Najeriya 36 (NGF) ta ƙagara ta ga an samu masalaha a rigimar wacce ta shiga tsakanin gwamna Similanayi Fubara da Nyesom Wike.
A cewarsu, tsoma baki da nufin sasanta rikicin wanda shugaban ƙasa ya kudiri aniya ya zama tilas domin guje wa yaɗuwar matsalar zuwa wasu jihohin, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A nasa ɓangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce ba shi da dalilin da zai sa ya yi katsalandan a harkokin mulkin Rivers, domin ya yi wa al’ummarta hidima na tsawon shekaru takwas.
Ya ci gaba da cewa babban abin da ya takaita a kai shi ne kare tsarin siyasar da aka gina tun shekarar 2015 a jihar Ribas.
Gwamnonin PDP sun jero dalilansu na goyon bayan Tinubu
Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kare tsoma bakin da Shugaba Tinubu ya yi a rikicin.
Saɓanin yadda wasu jiga-jigan da ke tare da Atiku Abubakar ke ikirarin cewa goyon bayan Tinubu na iya tarwatsa PDP, Bala ya ce yunƙurin ya yi daidai da ajendar NGF.
Darakta Janar na ƙungiyar gwamnonin PDP, CID Maduabum, shi ne ya faɗi haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin da gwamnan Bauchi ya dauka abin alfahari ne.
Ya kara da cewa shiga taakanin da Tinubu ya yi a Ribas da rashin tsoma bakinsa a cikin shari’ar kotunan zabe abin yabawa ne, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Sanarwan ta ce:
"Dukkan gwamnonin jihohi 36 sun goyi bayan yunƙurin, musamman Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Bala Mohammed, ya nuna goyon bayansa ga matakin Tinubu na shiga tsakani."
Kotu ta umurci a saki Emefiele
A wani labarin kuma Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Ta ce a sake shi ba tare da gindaya masa wasu sharuɗɗa ba, inda ta umarci EFCC da shugaban hukumar su aiwatar da wannan umarni.
Asali: Legit.ng