"Yaran Tinubu ne": Atiku Ya Caccaki Gwamnonin PDP Bisa Shiga Tsakani a Rikicin Wike, Fubara

"Yaran Tinubu ne": Atiku Ya Caccaki Gwamnonin PDP Bisa Shiga Tsakani a Rikicin Wike, Fubara

  • Ɗan takarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar, ya ce Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara, ba ƴan PDP ba ne
  • Abdulrasheed Shehu, mai magana da yawun Atiku ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake kare cewa mai gidansa ba zai sa baki a rikicin siyasar jihar Rivers ba
  • Kakakin na Atiku ya ƙara da cewa Wike da Fubara yaran shugaban ƙasa Bola Tinubu ne, kuma babu laifi idan sun nemi ɗauki a fadar shugaban ƙasa

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tsokaci kan rikicin siyasar jihar Rivers da kuma rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.

Abdulrasheed Shehu, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Atiku, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba zai tsoma baki a rikicin ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Atiku ya caccaki gwamnonin PDP
Atiku ba zai sanya baki a rikicin da ke tsakanin Wike, Fubara ba Hoto: Nyesom Wike, Atiku Abubakar, Sim Fubara
Asali: Twitter

Abdulrasheed ya yi nuni da cewa manyan ƴan siyasar guda biyu, masu biyayya ne ga Shugaba Tinubu ba Atiku ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar hadimin na Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya tsoma baki a lokacin da rikici ya ɓarke a tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu a jihar Edo, kuma jihar yanzu tana cikin kwanciyar hankali.

Meyasa Atiku ba zai sa baki a rikicin Wike da Fubara ba?

Sai dai, Shehu ya yi nuni da cewa, shi mutunci samunsa ake yi, inda ya ƙara da cewa idan har Wike da Fubara suka ƙi amincewa da shugabancin Atiku a jam'iyyar PDP, bai dace tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sa baki a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers ba.

Daga nan sai Shehu ya caccaki matakin gwamnonin PDP na ganawa da Wike a ofishinsa da ke Abuja domin magance rikicin jihar, inda ya ce ministan ya raina gwamnonin a taron manema labarai da ya yi bayan ganawarsu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wata hubbasa a rikicin siyasar Wike, Fubara

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"Wike da Fubara ba ƴan PDP bane. Su yaran Tinubu ne. Ba laifi da suka garzaya wurinsa. Matsalar ɗaya ce gwamnonin PDP da suka cusa kansu a wajen Wike, sannan kun ga yadda ya raina su a gaban idon su."

Wike Ya Fadi Silar Rikicinsa da Fubara

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana silar rikicinsa da Gwamna Fubara.

Wike ya yi nuni da cewa gwamnan ya fara ture masa ginin siyasar da ya kafa a jihar Rivers, wanda hakan ba abu bane wanda zai lamunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng