Wike Ya Lissafa Manyan Zunubai 3 Da Gwamna Fubara Ya Aikata Da Yasa Yake So a Tsige Shi

Wike Ya Lissafa Manyan Zunubai 3 Da Gwamna Fubara Ya Aikata Da Yasa Yake So a Tsige Shi

  • Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana matsalolin da ke tsakaninsa da magajinsa
  • Ministan Abujan ya bayyana cewa ba zai bari makiyansa na kusa da shi su karbe tsarin siyasar Ribas ba
  • Kamar yadda Wike ya bayyana, fadansa da gwamnan jihar bai da alaka da kudi illa yunkurin Fubara na son nuna shi ba komai bane a jihar Ribas da PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana dalilan da suka haddasa rigima tsakaninsa da magajinsa kuma tsohon na hannun damarsa, Siminalayi Fubara.

Wike ya fadi dalilin fadansa da Fubara
Wike Ya Lissafo Manyan Dalilai 3 da Suka Sa Yake Kulla-Kullan Tsige Gwamnan Ribas Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya lissafa dalilan fadansa da Fubara

Bayan ganawa da wasu gwamnonin PDP a Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, Mista Wike ya zargi Fubara da hulda da abokan hamayyarsa na siyasa, kamar yadda PremiumTimes ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike ya karyata rade-radi, ya shaidawa Gwamnoni silar rigimarsa da Gwamnan Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga taronsa da gwamnonin PDP, Wike ya bayyana cewa:

  1. Fubara na kokarin karbe ragamar ikon PDP a Ribas.
  2. Wike ya kuma bayyana cewa Fubara na aiki tare da makiyansa a jihar Ribas.
  3. Ministan Abuja ya kuma ambaci cewa Fubara na aiki don shan kansa a jihar Ribas: yana abubuwa sabanin yarjejeniyarsu bayan ya yi aiki shi kadai don ganin ya ama gwamnan Ribas.

Ministan Abuja ya yi karin haske kan dalilan a kasa:

"Ba za ka yi aiki ba, sannan mutane su fara kawo makiyanka; wadanda suka yake ka lokacin da kake fadi tashi don mutumin ya hau karagar mulki. Babu mai yin haka", Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta nakalto ministan yana fadi.

Tsohon gwamnan, wanda ya karyata cewar yana neman kudi ne daga magajin nasa, ya bayyana cewa Mista Fubara na kokarin karbe ragamar iko na tsarin PDP a Ribas, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

"Ba matsala ne ba idan an samu rashin jituwa tsakanin ɗa da mahaifi", Gwamna Fubara

"Ni ba dan siyasa mara godiya bane amma kada ka taba tsarin siyasar jihar. Ba zan rufe idanuna ba," cewar Wike.

Kalli bidiyon Wike yana caccakar Fubara

Wike ya magantu kan rikicin Ribas

A baya mun ji cewa Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike ya ce babu wanda ya isa ya ture ginin siyasar da ya kafa a jihar Ribas.

A lokacin da ya zanta da Gwamnonin jihohin PDP da su ka ziyarce shi a ofishinsa a ranar Talata, ya Nyesom Wike ya bude masu bakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng