Gwamnonin PDP Sun Sa Labule da Ministan Bola Tinubu, Bayanai Sun Fito

Gwamnonin PDP Sun Sa Labule da Ministan Bola Tinubu, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shiga gana wa da Ministan Abuja, Nyesom Wike a ofishinsa da ke babban birnin tarayya
  • Wannan taro na cikin yunƙurin gwamnonin na lalubo hanyar maslaha kan rigimar siyasa da ta ɓarke a jihar Ribas
  • Gwamna Bala Muhammad na Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin ne ya jagorance su zuwa wurin Wike

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tawagar gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin ƙungiyasu na gana wa yanzu haka da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a ofishinsa da ke Abuja.

Gwamnonin sun sa labule da Wike ne karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed (Ƙauran Bauchi).

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Gwamnonin PDP Sun Sa Labule da Ministan Bola Tinubu, Bayanai Sun Fito Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Ƙauran Bauchi ya dira ofishin Wike da misalin ƙarfe 12:40 na tsakar rana yau Laraba tare da rakiyar takwarorinsa da suka haɗa da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Kara karanta wannan

"Ba matsala ne ba idan an samu rashin jituwa tsakanin ɗa da mahaifi", Gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta tattaro cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang, da takwaransa na jihar Taraba, Agbu Kefas, na cikin tawagar gwamnonin PDP da suka ziyarci Wike.

Sai dai jim kaɗan bayan isar gwamnonin, Wike ya jagorance su suka shiga ganawar sirri a ofishinsa da ke Garki a birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Menene dalilin wannam ganawa?

Gwamnonin sun sa labule da Wike ne a wani ɓangare na yunkurin sasanta rikicin siyasan da ya ɓarke a jihar Ribas tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokoki.

A ranar Litinin, majalisar dokokin jihar Ribas ta fara yunƙurin tsige gwamna Fubara daga kan madafun iko, lamarin da ake zargin Wike ne ya biyo masa ta nan.

Wannan batu ya ja hankalin ƴan Najeriya musamman mambobin jam'iyyar PDP, ganin yadda shi kansa gwamnan ya sha barkonon tsohuwa a hanyar zuwa majalisar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP za su gana da Ministan Tinubu kan muhimmin batu 1, bayanai sun fito

Majalisar dattawa ta amince da naɗin RECs 7

A wani rahoton na daban Bakwai daga cikin sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta ƙasa INEC da Bola Tinubu ya naɗa sun tsallake tantancewa a majalisa.

Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin da shugaban ƙasa ya musu a zaman ranar Laraba, an gano abinda ya sa ba a tabbatar da sauran 3 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262