Gwamnonin PDP Za Su Gana da Ministan Tinubu Kan Muhimmin Batu 1, Bayanai Sun Fito

Gwamnonin PDP Za Su Gana da Ministan Tinubu Kan Muhimmin Batu 1, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shirya ziyartar ministan Abuja har ofishinsa da nufin lalubo bakin zaren rikicin jihar Ribas
  • Sun cimma matsayar gana wa da Nyesom Wike ne a zaman da suka yi ranar Talata da daddare a birnin tarayya
  • Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin da majalisar dokokin jihar Ribas ta yi na tsige gwamna Similanayi Fubara

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum.

FCT Abuja - Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko a inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za su kai ziyara ga Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Gwamna Fubara da Ministan Abuja, Wike.
Yanzu-Yanzu: Gwamnonin PDP Za Su Gana da Ministan Tinubu Kan Muhimmin Batu 1, Bayanai Sun Fito Hoto: Similanayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa gwamnonin sun tsara zuwa su gana da Wike ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2023 a ofishin ministan da ke Garki a Abuja.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda: Abin da yasa jami'anmu suka watsa wa gwamna ruwan zafi da barkonon tsohuwa

Darakta janar na ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta Najeriya, CID Maduabum, shi ne ya tabbatar da tsara wannan taro a wata sanarwa da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Maduabum, Gwamnonin sun cimma matsayar kai wa Wike ziyara ta musamman a taron da suka gudanar na ƙarshe a Abuja ranar Talata, 31 ga watan Oktoba.

Dalilin shirya wannan taro

Ya ce wannan zama da za a yi zai maida hankali ne kan yadda za a sasanta rigingimun da suka ɓarke a jihar Ribas tsakanin gwamna Similanayi Fubara da majalisar dokoki.

Wannan na zuwa ne awanni ƙalilan bayan gwamnan da Wike sun haɗu a wurin wani taro a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Talata.

Yayin haɗuwar tasu dai an ga manyan jiga-jigan biyu sun miƙa wa juna hannu sun gaisa cikin farin ciki da annashuwa, kana suka tattauna wanda ba a san me suka ce ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP aƙalla 4 sun sa labule da Ministan Tinubu a Abuja, bayanai sun fito

Tinubu ys shiga tsakani

Haka nan kuma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani kan wannan taƙaddama, ya gana da gwamna Fubara da Wike a Villa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito

Rikicin dai ya faro ne tun daga ranar Litinin, lokacin da majalisar dokokin jihar Ribas ta fara yunkurin tsige Fubara daga kujerar gwamna.

Jam'iyyar PDP zata shiga tsakani

A wani rahoton na daban Jam'iyyar PDP ta sanya baki a rigimar da ta ɓarke tsakanin Gwamnan Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas.

A wata sanarwa da ta wallafa ranar Talata, PDP ta buƙaci masu hannu a rikicin su bada damar yin sulhu don magance matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262