Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Sanatan Kogi Ta Tsakiya
- Natasha Akpoti-Uduagan ta yi nasara a shari'ar da ake yi da ita a kotun daukaka kara kan kujerar sanatan Kogi
- A ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, kotun ta ayyana yar takarar ta PDP a matsayin wacce ta lashe zaben Fabrairun 2023 na sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya
- Kotu ta yi fatali da karar da ke kalubalantar nasararta wanda babban abokin hamayyarta, Abubakar Ohere na APC ya shigar saboda rashin inganci
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara reshen Abuja, ta yanke hukunci mai ban mamaki kan shari'ar APC a jihar Kogi.
Kotu ta yi fatali da karar da aka daukaka don kalubalantar nasarar Natasha
Kotun koli: Jerin sunayen sanatoci da jiga-jigan PDP da su ka yi watsi da jam'iyyar bayan faduwar Atiku
A hukuncin da ta yanke a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, kotun ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin zababbiyar yar takara a kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya da aka yi a watan Fabrairun 2023, Channels TV ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da take zartar da hukuncinta, kotun ta yi watsi da karar da Abubakar Ohere ya shigar saboda rashin inganci, rahoton Sahara Reporters.
Yaya aka yi a kotun zabe?
A watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben jihar Kogi da ke zama a Lokoja ta soke nasarar Phere na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya.
Kotun ta kuma ayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta PDP a matsayin wacce ta lashe zaben sanatan na watan Fabarairu.
Sai dai kuma, Ohere ya tunkari kotun daukaka kara domin neman hakkinsa amma kuma gwamnatin ta sake tabbatar da Akpoti-Uduagan a matsayin ainahin wacce ta lashe zaben.
Tinubu ya ware N18bn na zaben jihohi 3
A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ware wa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INECC) naira biliyan 18 don gudanar da zabukan gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi wanda za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
A cewar ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, INEC za ta samu kudin ne daga cikin karin naira tiriliyan 2.1 (N2,176,791,286,033) na kasafin kudin 2023, jaridar The Nation ta rahoto.
Asali: Legit.ng