Ganduje da Gaske Yake, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani a Jihar Arewa

Ganduje da Gaske Yake, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani a Jihar Arewa

  • Jam'iyyar APC ta ƙara yi wa jam'iyyar PDP babban lahani yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a jihar Kogi
  • Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP da magoya bayansa, mambobin jam'iyyu uku sun sauya sheka zuwa APC
  • Mataimakin gwamna Yahaya Bello ya buƙaci su haɗa karfi da karfe wajen ɗaga martabar APC da kawo mata nasara

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Tsohon ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Dakta Joseph Erico, ya canza sheƙa zuwa All Progressives Congress (APC) ranar Litinin.

Erico, da tulin magoya bayansa sun shiga APC ne tare da ɗumbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyun SDP, Labour Party da APGA a wani gangami a filin taron Okpo da ke Olamaboro.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Jiga-Jigai sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kogi.
Mambobin Jam'iyyar PDP, SDP, LP da APGA Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kogi Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu sauya sheƙar sun samu tarba mai kyau daga mataimakin gwamnan jihar, Edward Onoja, a madadin gwamna Yahaya Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamna ya ja hankalinsu

Mista Onoja ya bayyana cewa wannan sauya sheƙa na nuni da ƙarshen ƴan adawa ya zo a jihar Kogi, inda ya kara da cewa za a basu wurin zama a APC mai mulki.

Ya kuma ba su tabbacin samun damarmaki daidai gwargwado, inda ya kwatanta tsohon jigon PDP a matsayin wani kadara, idan aka yi la’akari da kwarewarsa.

Mataimakin gwamnan ya roƙi gungun jiga-jigan da suka sauya shekar da su haɗa ƙarfi da ƙarfe da sauran mambobi domin jam'iyyar APC ta samu nasara.

Yayin da yake jaddada cewa siyasa daga tushe ita ce siyasa, mataimakin gwamnan ya nuna muhimmancin Olamaboro a siyasar jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamna ya sa labule da manyan dattawan PDP da Sarakunan jiharsa, bayanai sun fito

Ya kuma bayyana fatan cewa jam'iyyar APC zata samu ƙuri'u masu yawa a yankin a zaɓe mai zuwa, Daily Post ta ruwaito.

Legit Hausa ta fahimci cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, hukumar zaɓe INEC za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihar Kogi da kuma jihohin Imo da Bayelsa.

Fubara ya sa labule da manyan dattawan PDP

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Ribas ya shiga taro da manyan ƙusoshin jam'iyyar PDP a gidansa na gidan gwamnati da ke Patakwal.

Wannan gana wa na zuwa ne yayin da wasu ƴan majalisar dokokin jihar suka fara yunkurin sauke shi daga kan kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel