Yanzu-Yanzu: Gwamna Ya Sa Labule da Manyan Dattawan PDP da Sarakunan Jiharsa, Bayanai Sun Fito
- Gwamnan jihar Ribas ya shiga taro da manyan ƙusoshin jam'iyyar PDP a gidansa na gidan gwamnati da ke Patakwal
- Wannan gana wa na zuwa ne yayin da wasu ƴan majalisar dokokin jihar suka fara yunkurin sauke shi daga kan kujerar gwamna
- Rigima ta balle a majalisar dokokin jihar Ribas ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, 2023 lamarin da ya haddasa ruɗani da tashin hankali
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gwamna Similanayi Fubara na gana wa yanzu haka da dattawan jam'iyyar People Democratics Party (PDP) a jihar Ribas.
A rahoton Vanguard, ana hasashen wannan taro ba zai rasa nasaba da yunƙurin wasu mambobin majalisar dokokin jihar Ribas, na tsige Fubara daga mulki ranar Litinin.
Bayanai sun nuna cewa taron na gudana yanzu haka a gidan mai girma gwamna da ke gidan gwamnatin jihar a Patakwal, babban birnin Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin waɗan da suka halarci wannan zama sun haɗa da Dattijo Ferdinand Alabaraba, shugaban ƙungiyar dattawan PDP da Chief Sergeant Awuse, shugaban majalisar sarakunan Ribas.
OCJ Okocha, babban lauya a Najeriya da kuma Bro Felix Obuah, daraktan yakin neman zaɓen Fubara/PDP a zaben 2023 duk sun halarci wannan taro na yau Litinin.
Majalisa ta naɗa sabon shugaba
Idan baku manta ba majalisar dokokin jihar Ribas ta shiga cikin ruɗani da rigingimu tuna samun labarin ana yunƙurin tsige gwamna Fubara.
Sai dai wasu mambobin majalisar da ke goyon bayan mai girma gwamna sun yi zama a gidan gwamnati, inda suka sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki.
Ehie Edison, wanda da farko aka dakatar daga matsayin shugaban masu rinjaye, shi ne mambobin suka zaɓa a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin.
Zulum ya hango matsala
A wani rahoton kuma Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce matuƙar ba a magance Boko Haram da ISWAP ba, zasu iya shafe taswirar Najeriya.
Gwamnan ya ce ƙungiyoyin ƴan ta'addan ka iya amfani da sansanonin ƴan gudun hijira a matsayin wurin ɗaukar mayaka.
Asali: Legit.ng