Rikici Ya Ƙara Tsanani, Ƴan Majalisa Sun Zaɓi Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP
- Mambobin majalisar dokokin jihar Ribas da ke goyon bayan gwamna Fubara sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki
- Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da majalisar ta fara yunƙurin tsige Fubara daga kan mulkin jihar Ribas ranar Litinin
- Ehie Edison, wanda a farko majalisar ta dakatar daga matsayin shugaban masu rinjaye, shi ne ya zama sabon kakaki
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
Jihar Ribas - Mambobin majalisar dokokin jihar Ribas masu goyon bayan gwamna Similanayi Fubara, sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokokin jihar.
Ehie Edison, wanda da farko aka dakatar daga matsayin shugaban masu rinjaye, shi ne mambobin suka zaɓa a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin.
Bayanai sun nuna cewa ƴan majalisun sun zaɓi sabon shugaban ne a wani zama da suka yi a gidan gwamnatin jihar Ribas da ke Patakwal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Siminalayi Fubara ya tabbatar da wannan ci gaban a wanin saƙon taya murna da ya wallafa a shafinsa na Manhajar X watau Tuwita ranar Litinin.
Wannan lamari wani yunƙuri ne daga bangaren mambobin majalisar da ke adawa da masu ƙoƙarin tsige Fubara daga kujerar Gwamnan jihar Ribas.
Rahotanni sun nuna cewa ƙusan ƴan majalisa 26 ne suka zabi Edison a matsayin sabon kakakin majalisar kana suka dakatar da tsohon shugabansu.
Da yake martani kan zaɓen sabon shugaban majalisa a shafinsa na X, Gwamna Fubara taya Ehie Edison, murna inda ya ce, "Ina taya ka murna kakakin majalisa."
Yadda aka cire shugaban masu rinjaye
Tun da farko dai, an samu labarin cewa kacaniya ta ɓarke a zauren majalisar dokokin jihar Ribas bayan kishin-ƙishin ɗin ana yunƙurin sauke Fubara daga kujerar Gwamna.
A zamansu na ranar Litinin, ƴan majalisar jihar sun sauke Honorabul Edison daga matsayin shugaban masu rinjaye.
Ba Tinubu ne ya ci zaɓen 2023 ba
A wani rahoton kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben watan Fabrairu, 2023, Atiku Abubakar, ya jaddada matsayarsa cewa ba Bola Tinubu ya lashe zaɓe ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk da Kotun Allah ya isa ta yanke hukunci, tarihi zai wanke shi sarai.
Asali: Legit.ng