Da Ɗumi-Ɗumi: "Ba Tinubu Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Ba" Atiku Abubakar Ya Yi Bayani
- Alhaji Atiku Abubakar ya nuna takaicinsa kan hukuncin da Kotun ƙolin Najeriya ta yanke a ƙarar da ya shigar makon da ya wuce
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk da Kotun Allah ya isa ta yanke hukunci, tarihi zai wanke shi sarai
- Atiku ya faɗi haka ne a wurin taron manema labarai na duniya kan hukuncin Kotun, wanda ya gudanar ranar Litinin a Abuja
Ahmad Yusuf, Editan Legit Hausa ya shafe shekaru yana kawo rahotanni kan al'amuran siyasa da harkokin yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben watan Fabrairu, 2023, Atiku Abubakar, ya jaddada matsayarsa cewa ba Bola Tinubu ya lashe zaɓe ba.
Atiku ya yi wannan furucin ne a sakateriyar PDP da ke Wadata Plaza, inda ya gudanar da taron manema labarai na duniya ranar Litinin. Legit Hausa ta bibiyi jawabin da ya yi.
Daily Trust ta rahoto Atiku na cewa hukuncin da Alƙalan Kotun ƙoli suka yanke kan ƙarar da ya ɗaukaka ya nuna cewa, "komai ya lalace a ƙasar nan."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran 'yan adawan ɗan shekara 76 a duniya ya bayyana cewa matsalolin da Najeriya ke fama da su sun zarce zaɓen shugaban kasa kawai.
Ya ce ƙwararan shaidu sun nuna a zahiri cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta karya dokar zaɓe wajen ayyana Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara.
A kalamansa ya ce:
"Hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke, duk da shi ne na ƙarshe ya nuna tabbas ba abin da ke tafiya daidai."
Meyasa Atiku ya yi rashin nasara a Kotu?
Idan baku manta ba, Kotun ƙolin Najeriya, ranar Alhamis da ta gabata, ta tabbatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa.
Jigon APC a Kudu maso Gabshin Najeriya, Okoye Francis, ya ce Atiku da Peter Obi sun yi rashin nasara a ƙarar da suka shigar saboda sun gaza gamsar da Kotu.
Ba zan gudu ba - Atiku
A wani rahoton kuma A karshe, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi martani kan hukuncin kotun koli.
Yayin ganawar da manema labarai wanda Legit ta bibibya, Atiku ya ce akwai tarun matsaloli a hukuncin da ta bai wa Bola Tinubu nasara a kotun koli.
Asali: Legit.ng