Babu Inda Zan Tafi, Atiku Ya Magantu Kan Mataki Na Gaba Bayan Hukuncin Kotun Koli
- A karshe, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi martani kan hukuncin kotun koli
- Atiku ya yi magana ne a yau Litinin 30 ga watan Oktoba yayin ganawa da manema labarai a Wadata Plaza da ke Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan kotun koli ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi martani kan hukuncin kotun koli da ta yanke a makon da ya gabata.
A yau Litinin 30 ga watan Oktoba, Atiku ya yi magana tun bayan yanke hukuncin inda ya ce ba zai gajiya wurin neman hakkinsa.
Meye Atiku ke cewa kan kotun koli?
Yayin ganawar da manema labarai wanda Legit ta bibibya, Atiku ya ce akwai tarun matsaloli a hukuncin da ta bai wa Bola Tinubu nasara a kotun koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya ce:
“Ba zan gajiya ba, kuma babu inda zan je, idan kuna tunanin zan gajiya, to ku manta kawai.
“Tsawon lokacin da zan dauka ina numfashi, zan ci gaba da gwagwarmaya da sauran ‘yan Najeriya don inganta dimukradiyya da bin doka.”
Wane shawari ya bai wa matasa kan kotun koli?
Ya kara da cewa gwawarmayar kwato ‘yancin Najeriya da ci gabanta ya rataya ne a wuyan matasa ma su jinni a jika.
Atiku ya soki hukuncin inda ya ce kotun kolin ta zubar da mutuncinta wurin halasta haram da satar kamanni da kuma coge yayin hukuncin.
Atiku ya caccaki kotun koli kan halasta haram da takardun bogi
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki hukuncin kotun koli da aka gudanar a makon jiya.
Atiku ya ce kotun ta halasta haram da satar kamanni har ma da takardun bogi wanda ya zubar mata da mutunci.
Ya ce tarihi zai tabbatar da gaskiyarsa komai dadewa kan gwagwarmaya da kuma neman 'yanci da ya ke yi a kasar komai dade wa.
Asali: Legit.ng