Kotun Koli: Najeriya Ce Ta Fi Yin Asara Ba Ni Ba, Atiku

Kotun Koli: Najeriya Ce Ta Fi Yin Asara Ba Ni Ba, Atiku

  • Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya caccaki hukuncin kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna takaicinsa kan yadda kotun ta ƙi karɓar sabbin hujjojin da ya kawo kan Shugaba Tinubu
  • Atiku ya bayyana cewa bai yi asara ba sakamakon hukuncin kotun ƙolin ba, hasalima Najeriya ce ta fi yin asara

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ce Najeriya a matsayin ƙasa ta lalace.

Wannan dai na zuwa ne kimanin sa'o'i 72 bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya shigar saboda rashin cancanta, tare da tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Babu inda zan tafi, Atiku ya magantu kan mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli

Atiku ya yi magana kan hukuncin kotun koli
Atiku ya yi magana kan hukuncin da kotun koli ta yanke Hoto: George Osodi
Asali: Getty Images

A hukuncin da shugaban kotun mai alƙalai bakwai, mai shari'a Inyang Okoro ya yanke, kotun ƙolin ta ƙi la'akari da takardun bayanan karatun Shugaba Tinubu da Atiku ya samo daga jami'ar jihar Chicago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya nemi ya gabatar da takardun matsayin sabuwar hujja da za ta tabbatar da zargin da yake na cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi amfani da takardun jabu.

Sauran alƙalan kotun, Uwani Aji, Mohammed Garba, Ibrahim Saulawa, Adamu Jauro, Abubakar Tijjani, da Emmanuel Agim, sun yarda hukuncin yin watsi da ɗaukaka ƙarar Atiku Abubakar.

Atiku ya yi martani kan hukuncin kotun ƙoli

Atiku wanda ya yi magana a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, ya ce Najeriya ce ta fi yin asara a hukuncin da kotun ta yanke, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa

A kalamansa:

"Babbar asara ba tawa ba ce, ta Najeriya ce. Idan kotun ƙoli ta nuna cewa laifi yana da kyau kuma ya kamata a ba shi lada, to Najeriya ta yi asara, kuma ƙasar ta lalace ba tare da la'akari da wanda ke shugabantar ta ba."

Atiku Ya Magantu Kan Mataki Na Gaba

A wani labarin, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana mataki na gaba da zai ɗauka bayan hukuncin kotun ƙoli.

Atiku ya bayyana cewa babu inda zai je kuma zai cigaba da ƙoƙarin ganin ya ƙwaci haƙƙinsa ba tare da ya gaji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng