INEC REC: Tinubu Ya Dauko ‘Yan APC, Zai ba Su Manyan Kujeru a Hukumar Zabe

INEC REC: Tinubu Ya Dauko ‘Yan APC, Zai ba Su Manyan Kujeru a Hukumar Zabe

  • Bola Ahmed Tinubu ya bada sunayen wasu wadanda za su zama manyan Kwamishinonin INEC da aka fi sani da REC
  • Idan majalisa ta amince da sunayen wadanda aka kawo, ‘yan siyasa da magoya bayan APC za su shiga hukuma mai zaman kan ta
  • Akwai mutanen Bola Tinubu a cikin wadanda ake so su zama REC, wannan mataki da aka dauka ya sabawa tsarin mulki

M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Akalla mutum biyu da su ka zama sababbin Manyan Kwamishinonin hukumar zabe na INEC da za a nada, ‘yan jam’iyyar APC ne.

Binciken Premium Times ya nuna cewa baya ga ‘yan APC da Bola Ahmed Tinubu ya zabo, akwai mutanensa da su ke shirin darewa kujerun REC.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 12 a Hukumar Kula Da Ma’aikatan Tarayya

TINUBU
Bola Tinubu da shugabannin APC Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu zai nada REC a INEC

Wadanda aka zaba domin su zama REC a INEC su ne: Etekamba Umoren (Akwa Ibom), Isah Ehimeakne (Edo) da Oluwatoyin Babalola (Ekiti).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai Abubakar Ma’aji (Gombe), Shehu Wahab (Kwara), Bunmi Omoseyindemi (Legas) sai Aminu Idris (Nasarawa) da kuma Mohammed Yelwa (Neja).

Kamar yadda labari ya zo a baya, ragowar sun hada da Anugbum Onuoha mai wakiltar Ribas da Isma’ila Moyi da zai wakilci jihar Zamfara.

Alakar sababbin RECs da Tinubu da APC

Umoren, Shaka, Omoseyindemi da Onuoha duk su na da alaka ta-kusa ko ta-nesa da shugaba Bola Tinubu, APC ko manyan jam’iyya mai mulki.

Umoren ‘dan jam’iyyar APC ne kuma na hannun daman Godswill Akpabio wanda shi ne shugaban ma’aikatan fada da yake gwamnan Akwa Ibom.

Idan aka duba shafin Facebook, za a fahimci Isah Shaka ya na cikin magoya bayan shugaban kasa, doka ba ta ce 'dan siyasa ya rike mukamin ba.

Kara karanta wannan

Jerin Shari’ar Zaben Shugaban Kasa Mafi Zafi da Aka yi Tun Daga 1979 Zuwa Yau

Bunmi Omoseyindemi wanda zai wakilci Legas ya na cikin yaran Tinubu tun 2001 a siyasa, haka abin yake tsakanin Onuoha da Nyesom Wike.

Nade-naden Tinubu a INEC

Da farko ana da labari Ajuri Ngelale ya fitar da sunayen mutane tara ne, daga baya kuma aka kara mutum guda a cikin jerin - Etekamba Umoren.

Haka zalika a karshe an cire sunayen irinsu Messrs Agbede (Ekiti), Bello (Gombe), Ilayasu (Kwara), Yahaya Bello (Nasarawa) da Dambo (Zamfara).

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng