Jam'iyyar APC da Binani Sun Bayyana Matakin Dauka Na Gaba Bayan Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Fintiri

Jam'iyyar APC da Binani Sun Bayyana Matakin Dauka Na Gaba Bayan Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Fintiri

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ƴar takarar gwamnanta Aisha Binani, ba su gamsu da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke ba
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa za ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar da nasarar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
  • Jam'iyyar da Binani sun yi nuni da cewa za su cigaba da neman ƙwato haƙƙinsu tun daga kotun ɗaukaka ƙara har zuwa kotun ƙoli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Adamawa - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ƴar takararta a zaɓen gwamnan jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ahmed (Binani) sun sha alwashin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun zaɓe ta yanke.

Kotun zaɓen dai ta yanke hukunci a ranar Asabar, 28 ga watan Oktoba, inda ta tabbatar da zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP.

APC da Binani za su daukaka kara
Jam'iyyar APC da Binani za su daukaka kara kan hukuncin da kotun zabe ta yanke a zaben gwamnan Adamawa Hoto: Abba Musa Ibrahim
Asali: Facebook

Sai dai, kuma jam'iyyar APC da Binani sun mayar da martani daban-daban, inda suka bayyana cewa ba za su tsaya a iya kotun zaɓen ba, inda za su tafi kotun gaba domin nemo amsoshin tambayoyinsu, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Yanke Hukunci

APC ta yi martani kan hukuncin zaɓen gwamnan Adamawa

Da yake mayar da martani kan hukuncin, shugaban jam'iyyar APC na jihar, Idris Shuaibu, ya ce hukuncin ya ba shi mamaki da jam’iyyar APC, amma ba su damu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shu’aibu ya ce jam’iyyar za ta haɗa kai da shugabancin jam'iyyar na ƙasa domin neman takardun yanke hukunci domin zuwa kotun ɗaukaka ƙara, saboda a cewarsa, “Wannan hukunci ba gaskiyar abin da mutanen jihar Adamawa suka zaɓa ba ne."

Da yake jawabi yayin wata tattaunawa da manema labarai, shugaban jam’iyyar APC na jihar ya godewa ƴaƴan jam’iyyar kan duk ƙoƙarin da suka yi tun daga farko har zuwa ƙarshen shari'ar a ranar Asabar.

"Babu shakka jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta mayar da hankali da kuma ƙudirin aniyar bin dukkanin hanyoyin da doka ta tanada domin ƙwato haƙƙin mu." A cewar Shuaibu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Kotu Ta Yanke Hukunci a Ƙarar Aishatu Binani Kan Zaɓen Gwamnan Adamawa

Menene abin da Binani ta ce kan hukuncin?

Da take magana kan lamarin, Binani ta ce duk da ba ta da iko kan abin da zai faru, amma ta tabbata za a yi amfani da dukkanin hanyoyin da suka dace wajen samun adalci a shari'arta.

"Ba batun Binani ba ne. Mataki na gaba shine aiki tare. Kotun zaɓe ita ce matakin farko, akwai kotunan ɗaukaka ƙara da ƙoli. Za mu sanar da matakai na gaba bayan tuntuɓa a kan lokaci, da yardar Allah." A cewarta.

Majalisa Ta Rantsar da Sabon Sanatan Adamawa

A wani labarin kuma, majalisar dattawa ta rantsar da Sanata Amos Yohanna na jam'iyyar PDP a matsayin sabon sanatan Adamawa ta Arewa.

Yohanna Amos ya maye gurbin Elisha Abbo na jam'iyyar APC bayan ya yi nasara a kansa a kotun zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng