Malamin Addini Ya Magantu Kan Damar Peter Obi Na Zama Shugaban Kasa a 2027
- Primate Elijah Ayodele ya ce tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ba zai iya zama shugaban kasa ba a 2027
- Primate Ayodele a ayyana cewa ba zai yi tasiri ba a siyasance a babban zaben Najeriya mai zuwa
- Malamin addinin ya ce ana iya kallon gazawar Obi wajen lashe zaben shugaban kasa a 2023 a matsayin "alheri"
Jihar Lagos - Fitaccen malamin addini, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi watsi da damar Peter Obi na zama shugaban kasa a babban zabe mai zuwa a 2027.
Primate Ayodele ya ce da Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben watan Fabrairun 2023, ya hade da Atiku Abubakar na PDP da bai fadi zaben ba.
"Obi ba zai iya zama shugaban kasa ba a 2027": Ayodele
Kamar yadda malamin addinin ya bayyana, idan Obi ya yanke shawarar sake takara a zaben 2027, kawai 'bata kudinsa zai yi'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Obi ba zai iya zama shugaban kasa a 2027 ba. Idan yana mafarkin haka, ya kamata ya manta kawai; magana ta gaskiya. Amma kana iya bata kudinka kuma. Ba kudina bane, kudinka ne.
"Za ka ga cewa ba za ka yi tasiri ba ko kadan a siyasance a 2027. Ba za su ganeka ba ko kadan. Duk wanda ke fada maka cewa ka dawo, haka za su dunga fada maka, 'yi wannan, yi wancan'.
"Wannan ya wuce. Dama ce ga Atiku da Obi, da sun hade. Za su lashe zaben (2023). Sannan kai (Obi) ba ka so jin gaskiya ba. Mun taya ka (Obi) murna kaima. Ba ka fadi ba, ka yi kokari sosai. Faduwa yana cikin alhairi."
Ganduje ya shawarci Atiku da Obi
A wani labari na daban, Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bukaci Atiku Abubakar da Peter Obi da su dauki na annabawa.
Ganduje ya shawarci manyan yan siyasar da su sake gwada sa’arsu a 2031. Lokacin zai yi daidai da kammala mulkin shugaban kasa Bola Tinubu na biyu.
Kotun koli dai ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Alhami,s 26 ga watan Oktoba inda ta yi fatali da kararrakin da sauran yan takarar shugaban kasa suka shigar.
Asali: Legit.ng