Kotun Koli: Jam’iyyar LP Ta Taya Tinubu Murna, Ta Aika Sako Ga Atiku
- Bangaren jam'iyyar LP da Lamidi Apapa ke jagoranta ta taya Shugaban kasa Bola Tinubu murn kan nasararsa a kotun koli
- Abayomi Arabambi, kakakin bangeran, a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, ya ce nasarar da Tinubu ya samu ya cancanta
- Arabambi ya kuma yi ba'a ga Peter Obi, yana mai cewa bai dauki alkalan kotun koli lokaci ba wajen yin fatali da karar da ya daukaka
FCT, Abuja - Bangaren jam'iyyar LP da Lamidi Apapa ke jagoranta ta taya shugaban kasa Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, bangaren LP din ta bukaci Shugaba Tinubu da ya zama mai karamci a nasara sannan ta nuna shirinta na shiga a dama da ita a sabuwar gwamnati.
Bangaren LP ta yi ba'a ga Peter Obi kan kayen da ya sha a kotun koli
Haka kuma, bangaren jam'iyyar ta yi ba'a ga dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, tana mai cewa ko awanni bai dauki alkalan kotun koli ba wajen yin fatali da karar da ya daukaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku tuna cewa a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, kotun koli ta yi fatali da kararrakin da Peter Obi da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar suka daukaka a kan nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Da yake martani ga hukuncin kotun koli a ranar Asabar, 28 ga watan Oktoba, Abayomi Arabambi, kakakin LP, ya ce Shugaba Tinubu ya cancanci nasarar da ya samu.
Bangaren LP ta bukaci Tinubu ya zama mai karamci cikin nasara
"Yanzu nasara ta samu a n kawo karshen dukkan takkadamar da suka taso daga zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu. Muna fatan cewa shugaban kasar zai nuna karamci cikin nasara ta hanyar gayyatar shugabancin LP domin a hada hannu wajen ci gaban gwamnatinsa na hadin kan kasa baki daya.
"Yayin da mu a jam'iyyar LP muke rokon wadanda suka sha kaye, musamman dan takarar shugaban kasa na PDP, da su nuna kishin kasa a matsayin yan damokradiyya, muna bukatan wanda ya lashe zaben da ya nuna karamci cikin nasarfa tun da gwamnatin tamu ce mu dukka."
Shugaban LP ya kori hadimansa
A wani labarin, mun ji cewa hugaban jam’iyyar LP, Barista Julius Abure ya fatattaki wasu daga cikin hadimansa.
Abure ya dauki wannan matakin ne kwanaki biyu bayan jam’iyyar ta sha kaye a kotun koli da ta bai wa Tinubu nasara.
Asali: Legit.ng