Kotu Ta Yanke Hukunci a Karar Aishatu Binani Kan Zaben Gwamnan Adamawa

Kotu Ta Yanke Hukunci a Karar Aishatu Binani Kan Zaben Gwamnan Adamawa

  • Babbar Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da Aishatu Binani ta nemi a dakatar da gurfanar da kwamishinan zaɓen Adamawa
  • Dakataccen kwamishinan, Hudu Ari, na fuskantar shari'a a gaban Kotu kan ayyana sakamakon zabe ba bisa ƙa'ida ba
  • Binani ta ce hukunta Ari zai yi wa ƙarar da ta shigar a Kotun zaɓe illa, amma duk da haka Alkali ya ce ba shi da hurumin sauraron ƙarar

FCT Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ƙarar da Aishatu Ɗahiru Binani, ƴar takarar gwamna a inuwar APC ta shigar kan zaɓen jihar Adamawa.

Premium Times ta ce a zaman ranar Jumu'a, Kotu ta yi watsi da karar Binani, wadda ta ƙalubalanci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da wasu.

Sanata Aishatu Binani.
Kotu Ta Yanke Hukunci a Karar Aishatu Binani Kan Zaben Gwamnan Adamawa Hoto: Aishatu Dahiru Binani
Asali: Twitter

A ƙarar dai Sanata Binani ta roƙi Kotu ta dakatar da INEC daga yunƙurin gurfanar da dakataccen kwamishinan zaɓen Adamawa, Hudu Yunusa Ari, saboda ya ce ita ta ci zaɓe.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Ƴar takarar APC da buƙaci kotu ta hana INEC ɗaukar mataki kan Hudu Ari har sai an yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da ta shigar gaban kotu sauraron ƙarar zaben gwamnan Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Binani, gurfanar da Hudu Ari a gaban babbar Kotu zai kawo mata cikas a shari'ar da ta shigar gaban Kotun zaɓe saboda kwamishinan ne babbar shedarta.

Wane hukunci Kotun ta yanke?

Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun ƙarƙashin mai shari'a Donatus Okorowo, ta yanke cewa ba ta da hurumin sauraron wannan ƙara, don haka ta kore ta.

Ta kuma bayyana cewa waɗan da ake ƙara sun yi nasara, ma'ana zasu iya gurfanar da dakataccen kwamishinan zaɓen ba tare da wata matsala ba.

Idan baku manta ba, bayan Hudu Ari ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan Adamawa, INEC ta ƙasa ta haramta masa shiga ofishin jihar.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Bayan ƙarisa zaben da ya rage, hukumar INEC ta ayyana Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen kana ta umarci a gaggauta hukunta Mista Ari, The Cable ta ruwaito.

Falana ya yi magana kan hukuncin Kotun ƙoli

A wani rahoton na daban Babban lauya a Najeriya mai fafutukar kare hakkin ɗan adam, Femi Falana ya yi magana kan nasarar da Bola Tinubu ya samu a Kotun ƙoli

Falana ya bayyana cewa bai kamata ace ɓangaren shari'a ne zai tantance wanda ya ci zaɓe ba idan har INEC ta yi aikinta yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262