Falana Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotun Koli Na Tabbatar da Nasarar Tinubu a 2023

Falana Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotun Koli Na Tabbatar da Nasarar Tinubu a 2023

  • Babban lauya a Najeriya mai fafutukar kare hakkin ɗan adam, Femi Falana ya yi magana kan nasarar da Bola Tinubu ya samu a Kotun ƙoli
  • Falana ya bayyana cewa bai kamata ace ɓangaren shari'a ne zai tantance wanda ya ci zaɓe ba idan har INEC ta yi aikinta yadda ya dace
  • Ya ce sakamakon zaben 2023 ya nuna karara cewa Najeriya na da jan aiki a gabanta game da tsarin zabenta

Fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Femi Falana (SAN) ya ce ko kaɗan bai kamata a ce shari'a ce zata warware sakamakon zaben Najeriya ba idan har hukumar zaɓe ta tsaftace aikinta.

Falana ya yi wannan furucin ne ranar Jumu'a, 27 ga watan Oktoba, 2023 a wata hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirin nan na su 'Siyasa a yau'.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Shugaba Tinubu tare da Femi Falana SAN.
Falana Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotun Koli Na Tabbatar da Nasarar Tinubu a 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Femi Falana
Asali: Facebook

Babban lauyan ya yi waɗannan kalamai ne yayin da aka tambaye shi ya faɗi matsayarsa kan hukuncin da Kotun ƙolin Najeriya ta yanke ranar Alhamis.

Kotun ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu bayan ta cure karar Atiku da ta Peter Obi wuri ɗaya, ta yi watsi da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falana ya maida martani

Da yake martani kan hukuncin, Falana ya ce:

"Ba wai shari’a ta goyi bayan zaben da INEC ta gudanar bane. Duk da hukuncin, a fili yake cewa Najeriya na da jan aiki a gabanta wajen ganin an gudanar da sahihin zabe."
"Zaben da ba za a yi tashe-tashen hankula ba, zaben da dukkan mu za mu yi alfahari da shi. Amma har yanzu muna da jan aiki kafin mu cimma wannan mataki, ko da hukuncin Kotu."

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Kan Hukuncin Kotun Ƙoli

Falana ya zargi INEC da gazawa, yana mai cewa da sun yi aikinsu yadda ya kamata, da ba za a ɗora wa Kotun ƙoli alhakin tabbatar da sahihin wanda ya samu nasara ba.

"Bai kamata a ce shari'a ce zata bayyana waɗanda suka lashe zaɓe ba, ba alƙalai ke da alhakin tabbatar da waɗanda suka ci zaɓe ba. Wannan nauyi ne da ke kan INEC idan ta yi abinda ya kamata."
"Shiyasa ya zama wajibi mu kawo ƙarshen wannan abun kunyar wanda ya zama doka a batun gudanar da zaɓen mu."

Atiku ya fito bainar jama'a

A wani rahoton kuma Tun da Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, aka daina jin ɗuriyar Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fito a karon farko inda ya nuna cewa ya halarci ɗaura aure a babban Masallacin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262