Atiku Abubakar Ya Bayyana Karon Farkon Bayan Rashin Nasara a Kotun Koli
- Tun da Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, aka daina jin ɗuriyar Atiku Abubakar
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fito a karon farko inda ya nuna cewa ya halarci ɗaura aure a babban Masallacin ƙasa
- Har yanzu Wazirin Adamawa bai ce komai ba kan hukuncin ba kuma ana ta kiran ya fito ya taya shugaba Tinubu murna
FCT Abuja. - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya fito bainar jama'a a karon farko a babban masalllacin ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Wannan ne karon farko da Atiku ya fito har mutane suka ganshi tun bayan hukuncin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke kan zaɓen shugaban ƙasa 2023.
Idan baku manta ba, Kotun wacce ake wa taken daga ke sai Allah ya isa ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Fitowarsa ta karshe ita ce a taron manema labarai na ƙasa da ƙasa wanda ya gudanar a cibiyar ‘Yar’Adua da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Atiku ya fito yi?
Wasu Hotuna da Legit Hausa ta ci karo da su a shafin Manhajar X, Atiku ya halarci ɗaurin auren ɗiyar muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagun.
Yayin da yake tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita, Alhaji Atiku ya ce:
"A babban Masallacin ƙasa kenan bayan Sallar Jumu'a tare da wasu manyan jiga-jigai, mun yi addu'a yayin ɗaura auren ɗiyar muƙaddashin shugaban jam'iyyar PdP, Umar Damagun"
Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton, Atiku bai taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, murna ba duk da kiraye-kirayen wasu ƙungiyoyi na ya yi hakan.
Daga cikin waɗanda suka shawarci Atiku ya taya shugaban ƙasa murna har da tsohon sanatan PDP, Ben Murray-Bruce; da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.
Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugaban matasanta na jihar Ondo jim kaɗan bayan rashin nasarar Atiku Abubakar a Kotun ƙoli.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, PDP reshen jihar ta umarci ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin a bincike shi.
Asali: Legit.ng