Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ce kwarewarsa a wajen rawa ya sa mutane da dama suna yi masa kallon ba zai iya ba bayan ya hau mulki
  • Adeleke ya ce ya bai wa masu sukarsa mamaki da tarin kokarin da ya yi wa jihar bayan ya karbi mulki daga hannun Gbenyega Oyetola
  • Gwamnan ya kaddamar ayyukan samar da ababen more rayuwa na naira biliyan 100 a fadin jihar, wadanda ya ce za a kammala cikin watanni 12

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana cewa mutane da dama sun yi masa kallon wanda zai gaza lokacin da aka rantsar da shi.

Adeleke ya ce an yi masa kallon ba zai iya ba saboda kwarewarsa a bangaren rawa, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Da Ya Ziyarci Tinubu Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Ya Fadi Dalilin Ziyarsa

Gwamna Adeleke ya ce mutane da yawa sun raina shi a lokacin da aka rantsar da shi
Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a lokacin kaddamar da ayyukan samar da ababen more rayuwa na naira biliyan 100 a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba.

Wasu ayyuka Gwamna Adeleke ya yi?

Gwamnan ya bayyana cewa sai dai kuma, ya shayar da masu sukansa mamaki da irin kokarin da ya yi tun bayan da ya karbi ragamar shugabanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Adeleke ya bayyana, an yi amfani da watanni 11 da suka gabata wajen magance sama da kashi 90 cikin 100 na lalacewar ababen more rayuwa da gwamnatinsa ta gada.

Ya bayyana cewa za a gyara cibiyoyin kiwon lafiya 345 sannan za a gina rijiyoyin burtsatse 332.

Adeleke ya kara da cewa, za a gina tituna 45 mai tsawon akalla kilomita daya a fadin kananan hukumomi 30, wanda hakan ke nufin za a gyara hanyoyi masu tsawon kilomita 45, za yi tagwayen hanyoyi a Osogbo, Ede da Ilesha.

Kara karanta wannan

“Ina Samu a Wajen Wata Matar”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ke Hana Shi Hakkinsa Na Aure

Ya ce:

"Za mu gina gadar sama guda biyar don saukaka afkuwar hatsarurruka da cunkoso. A Oshogbo (2), daya a Ikirun, daya a Ife sannan daya a Owode-Ede da sauran ayyuka.
"Za a kammala dukkanin ayyukan nan a cikin watanni 12 da yardar Allah. Saboda haka ina mai alfaharin kaddamar da ayyukan samar da ababen more rayuwa na biliyoyin naira a Osun."

Gwamna ya hana jami'an gwamnati fita waje

A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya soke fita kasashen waje ga dukkan mukarraban gwamnatinsa a jihar.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne don rage yawan kashe kudade ganin yadda jihar ke fama da karancin kudi a halin yanzu, cewar The Nation.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng