Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Dokoki Na PDP a Edo

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Dokoki Na PDP a Edo

  • Destiny Enabulele na jam'iyyar PDP ya sha kaye a hannun Sunday Aghedo na APC a kotun zabe
  • Kwamitin kotun zabe mai mutum uku ya tsige Enabulele saboda rashin bin dokar zabe na 2022
  • Mai shari'a A.O Chijoke ya ayyana Aghedo a matsayin wanda ya lashe zabe sannan ya umurci INEC da ta janye satifiket din Enabulele sannan ta ba dan takarar na APC

Jihar Edo - Kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige dan majalisa na jam'iyyar PDP, Destiny Enabulele, wanda ke wakiltan mazabar Ovia ta kudu maso yamma a majalisar dokokin jihar Edo.

Kwamitin kotun zaben mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari'a A.O Chijoke, ya ayyana Sunday Aghedo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Wamakko a Matsayin Sanatan APC

Kotun zabe ta tsige mamban PDP a majalisar jihar Edo
Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Dokoki Na PDP a Edo Hoto: Ojo Evans / Omuwa Godswill
Asali: Facebook

Me yasa kotu ta tsige Enabulele?

Da take yanke hukunci a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba a garin Benin, kotun zaben ta tsige Enabulele kan kin bin ka'idar dokar zaben 2022, kamar yadda aka gyara ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta ba Enabulele sannan ta bai wa Aghedo.

Enabulele ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Ovia ta kudu maso yamma.

Kotun zaben ta isa ga hukuncin inda ta cire kuri'u 1000 daga kuri'un da aka bai wa Enabulele, wanda alkalan suka bayyana a matsayin marasa inganci.

Aghedo NA apc ya yi ikirarin cewa an samu zartawar kuri'u da razana magoya bayansa.

Babban lauyan Aghedo, Famous Osawaru, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga damokradiyya ga tsarin doka.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Ganduje Ya Bayyana Shekarar da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi Takarar Shugaban Kasa

Kotu ta tabbatar da nasarar Wamakko

A wani labarin, mun ji cewa kotun sauraran kararrakin zaben ‘yan majalisu ta yanke hukunci kan zaben Sanata Aliyu Wammako na jihar Sokoto.

Kotun ta yi fatali da korafe-korafen tsohon mataimakin gwamna, Manir Dan’iya na jam’iyyar PDP mai adawa a kasar. Wamakko na wakiltar Sokoto ta Arewa karkashin jam’iyyar APC mai mulki yayin da Dasuki ke jam’iyyar PDP, cewar Punch.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a, Josephine Oyefeso a madadin sauran alkalan ta tabbatar da zaben Wamakko tare da fatali da korafe-korafen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng