Jerin Shari’ar Zaben Shugaban Kasa Mafi Zafi da Aka yi Tun Daga 1979 Zuwa Yau

Jerin Shari’ar Zaben Shugaban Kasa Mafi Zafi da Aka yi Tun Daga 1979 Zuwa Yau

Abuja - ‘Yan takara sun saba shigar da kara a kotun korafin zabe idan ba su yi nasara ba, haka lamarin yake a siyasar Najeriya.

Rahoton nan ya nutsa tarihin takarar shugaban kasa, ya kawo shari’o’i masu zafi da aka yi.

M. Malumfashi ya kan kawo labarai na Hausa musamman na siyasa, addini, wasanni da al’ada

1. Shari'ar zaben 1979 (Shehu Shagari v Obafemi Awolowo)

Tarihi ya nuna a shari’ar zaben 1979, an kai ruwa-rana wajen fassara sashe na 34 A (I), lauyoyin Obafemi Awolowo ba su yarda Shehu Shagari ya yi nasara a kan shi ba.

Abin da ya jawo sabani shi ne yadda za a fassara samun nasara a biyu bisa ukun jihohin kasar (a wancan lokaci jihohi 19 ake da su), Shagari da NPN su ka yi galaba.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Shugaban kasa
Labarin shari'ar zaben shugaban kasa Hoto: Reuters, www.sandiegouniontribune.com, tribuneonlineng.com, Asiwaju Bola Tinubu
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ya sabawa hukunci mai rinjaye shi ne Kayode Aso, Atanda Fatai Williams, Mohammed Bello, Mohammed Uwais, Andrew Otutu sun tafi a kan ra’ayi guda.

Sauran Alkalan da su ka saurari shari’ar zaben su ne Ayo Gabriel Irikefe da Chike Idigbe.

2. Shari'ar zaben 2007 (Umaru Yar’Adua v Muhammadu Buhari)

Bayan nasarar PDP a zaben shugaban kasa na 2007, Muhammadu Buhari (ANPP) da Atiku Abubakar (ACN) sun shigar da kara a kotun korafin zabe, amma ba su dace ba.

Da aka je kotun koli, Alkalai bakwai da su ka saurari korafin sun samu rabuwar kai. Wasu Alkalan sun ce magudin da aka yi ya isa a dakatar da zaben na 2007.

VOA ta ce Nike Tobi da Alkalai hudu sun ce lauyoyin ‘yan adawa ba su kawo hujjojin kwarai ba, George Oguntade a madadin alkalai uku ya ce an yi murdiya a zaben.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Gbajabiamila, Nuhu Ribadu Sun Hadu da Lauyan Atiku a Kotun Koli, Hoto Ya Bayyana

3. Shari'ar zaben 2019 (Muhammadu Buhari v Atiku Abubakar)

Mohamed Garba ya karbi shari’ar farko na zaben 2019 daga hannun Zainab Bulkachuwa, an dauki kwanaki 177 kafin ayi hukunci tsakanin Buhari v Atiku.

Lauyoyin ‘dan takaran PDP sun yi ikirarin Buhari da APC ba su ci zabe ba, kuma su ka jefe shi da rashin takardun karatu, aka kawo maganar Atiku ba ‘dan kasa ba ne.

Shugaba Buhari ne ya yi nasara a kotun korafin zabe, da aka je kotun koli, Mai shari’a Tanko Muhammad ya sake watsi da rokon jam’iyyar PDP, ya ba APC nasara.

4. Shari'ar zaben 2023 (Bola Tinubu v Atiku Abubakar & Peter Obi)

A makon nan Alkalan Kotun Koli su ka yanke hukunci a shari’ar Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, an tabbatar da jam’iyyar APC ta ci zaben shugaban kasa.

John Inyang Okoro ya jagoranci sauraron shari’ar takarar 2023 ya kuma yi watsa-watsa da korafin masu kara, duk da wahalar da Atiku Abubakar ya sha a Amurka.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Fadawa Abba Gida Gida Ya Shirya, APC Za Ta Karbe Mulkin Kano a Kotu

Kotun kolin ba ta karbi sababbin hujjoji game da takardun Tinubu ba, kuma ta ba kotun korafi gaskiya kan hukuncin amfani da IREV da samun 25% na kuri’un Abuja.

Rarara ya caccaki Buhari

Ana da labari Dauda Adamu Kahutu da aka fi sani da Rarara ya fito ya na sukar Muhammadu Buhari bayan nasarar Bola Tinubu a kotun koli.

Bashir Ahmaad wanda ya yi aiki da tsohon shugaban ya aika masa martani a Facebook, ya ce hankali ba zai dauki maganganun mawakin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng