"Shari'a Ta Kare, Ku Zo Mu Hadu a Gina Shugabanci Na Gari" Sanata Barau

"Shari'a Ta Kare, Ku Zo Mu Hadu a Gina Shugabanci Na Gari" Sanata Barau

  • Sanata Barau Jibrin ya jinjina wa Alkalan Kotun ƙoli bisa hukuncin da suka yanke na tabbatar nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya roƙi masu kara, Atiku da Obi, su haɗa hannu da Tinubu don ci gaban ƙasa
  • A yau Alhamis, Kotun daga ke sai Allah ya isa ta kori kararrakin Atiku na PDP da Peter Obi na Labour Party

FCT Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da hukuncin Kotun ƙoli wanda ya tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Sanata Barau ya nuna murna da hukuncin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismail Mudashir, ya fitar ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
"Shari'a Ta Kare, Ku Zo Mu Hadu a Gina Shugabanci Na Gari" Sanata Barau Hoto: Senator Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga Demokuraɗiyya kana ya roƙi Atiku da Peter Obi su dawo su haɗa hannu da shugaba Tinubu domin magance matsalolin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan Hukuncin Kotun Koli, Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Sabon Naɗin da Tinubu Ya Yi

A ranar Alhamis kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi suka shigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau ya yi magana kan hukuncin Kotu

A sanarwan, mataimakin shugaban majalisar dattawa ya roƙi masu kara da su rungumi wannan hukunci na gaskiya da Kotu ta yanke hannu bibbiyu.

Ya kuma jinjina wa Alkalan Kotun bisa tabbatar da zaɓin masu kaɗa kuri'a, waɗan da suka dangwala wa shugaba Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu.

A rahoton The Nation, Sanata Barau ya ce:

“Batun shari’a ya kare bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a yau, wanda ke tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023."
‘"Yan Najeriya sun yi nasara, dimokuradiyya ta yi nasara, kuma hakan zai yi wa ƙasar nan kyau. Ina yaba wa alkalan kotun koli bisa tabbatar da muradin ‘yan Najeriya wadanda suka zabi shugaba Tinubu a lokacin zaben 2023."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Watsi da Bukatar Atiku Ta Shigar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu

"Lokaci ya yi da kowa zai hada kai da shugaban kasa don aiwatar da manyan tsare-tsare da manufofinsa na ci gaban kasarmu domin tabbatar da ajandar sabunta fata."

Majalisa ta tabbatar da naɗin shugaban ICPC

A wani rahoton kuma Musa Aliyu ya zama cikakken shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC bayan tantance shi a majalisar Dattawa.

Majalisar ta amince da naɗinsa a zamanta na ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023, bayan Sanata Barau Jibrin ya jagoranci tantance shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel