Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Nadin Sabon Shugaban Hukumar ICPC Ta Ƙasa
- Musa Aliyu ya zama cikakken shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC bayan tantance shi a majalisar Dattawa
- Majalisar ta amince da naɗinsa a zamanta na ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023, bayan Sanata Barau Jibrin ya jagoranci tantance shi
- Idan kuna biye, jiya Laraba shugaban ƙasa ya tura saƙo ga majalisar inda ya nemi ta gaggauta amince wa da naɗin sabon shugabam ICPC
FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Musa Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC).
Jaridar Punch ta tattaro cewa an tabbatar da naɗinsa ne jim kaɗan bayan tantance shi a zaman majalisar na yau Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023.
Majalisar ta fara aikin tantance Aliyu ne da misalin ƙarfe 11:50 na safiya bayan shugaban masu rinjaye, Bamidele Opeyemi, ya nemi a ɗage dokar majalisar domin barin baƙi su shigo.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu Ƙoli, Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi
Kwamitin da ya kunshi baki ɗaya mambobin majalisar dattawa ne ya tantance Aliyu, wanda ya kasance lauya masanin doka kuma Antoni Janar na jihar Jigawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, mataimakin shugaban majalisar Dattawa ne ya jagoranci tantance sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ICPC, The Nation ta ruwaito.
Tinubu ya aika sako ga majalisa
Idan baku manta ba a jiya Laraba shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura sako ga majalisar, inda ya roƙi ta hanzarta tabbatar da Musa Aliyu a matsayin shugaban hukumar.
Wannan ya biyo bayan sanarwan naɗin Aliyu wadda mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar sama da mako ɗaya da ya shuɗe.
A cewar Ajuri, an yi nadin ne “domin ci gaba da sabunta fatan yan ƙasa da sake fasalin manyan cibiyoyi da kuma karfafa yakin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa.”
Ya ce naɗin ya biyo bayan tafiya hutun da tsohon shugaban hukumar ya yi wanda wa'adinsa zai ƙare a watan Fabrairun shekara mai zuwa 2024.
"Obi ba zai taɓa zama shugaban ƙasa ba"
A wani rahoton kuma Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya cika da murna kan faduwar Peter Obi a kotun koli.
Omokri ya ce Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.
Asali: Legit.ng