Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Watsi da Bukatar Atiku Ta Shigar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu
- Kotun ƙoli a yayin zamanta na ranar Alhamis, ta kawo cikas ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar
- Kotun ƙolin ta ƙi amincewa da buƙatar Atiku ta gabatar da sabbin hujjoji kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- A cewar kotun, lokacin yin hakan ya riga da ya wuce saboda haka ba za ta amsa buƙatar shigar da sabbin hujjojin ba
FCT, Abuja - Kotun koli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, ta yi watsi da rokon Atiku Abubakar na gabatar da sabbin shaidu kan shugaban ƙasa Bola Tinubu.
A cewar gidan talabijin na Channels tv, kotun ƙoli ta gaya wa Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP cewa kwanaki 180 da aka ba su damar samun sabbin shaidu sun wuce.
Mai shari’a Inyang Okoro ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis yayin sauraron ƙarar da aka ɗaukaka kan nasarar Bola Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban ƙasa (PEPC).
Atiku na son kawo sabbin hujjoji
Atiku dai ya garzaya kotun ne domin ta bashi izinin kawo ƙarin hujjojin da za su tabbatar da cewa Tinubu ya miƙa takardar shaidar jabu ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi iƙirarin cewa Tinubu ya miƙa wata takarda mai cike da alamun tambaya wacce ke nuna cewa ya kammala karatunsa daga jami'ar jihar Chicago (CSU) ga INEC a shekarar 2023.
Lauyan Atiku, Chris Uche (SAN), ya ce takardun masu shafuka 32 da aka ba wanda yake karewa a Amurka, ya kamata kotun ta karɓe su domin yin adalci.
Sai dai kotun ƙolin ta ƙi amincewa da hakan kuma ta ce wa'adin da za a shigar da irin wannan hujjar ya wuce, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
CJN Ariwoola Ya Amince a Haska Zaman Kotun Koli
A wani labarin kuma, alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), Olukayode Ariwoola, ya amince a haska zaman kotun ƙoli na yanke hukunci kan sauraron ƙararrakin da Atiku da Peter Obi suka ɗaukaka kan nasarar Shugaba Tinubu.
Ariwoola ya amince da hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoban 2023, a yayin da ake shirin zartar da hukunci kan ƙararrakin.
Asali: Legit.ng