Tinubu Ya Nada Munirudden, Akutah a Matsayin Daraktocin Hukumar NIWA, NSC
- Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a ma'aikatar Albarkatun Ruwa karkashin jagorancin minista Adegboyega Oyetola
- Tinubu ya nada Munirudden Bola Iyebamiji daraktan hukumar NIWA da Akutah Ukeyima na hukumar NSC
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai ta zamani, David Olusegun shi bayyana haka a yau Laraba a shafin X
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Shugaba Tinubu ya nada manyan mukamai guda biyu a ma'aikatar Albarkatun Ruwa.
Tinub ya yi wannan nadin bayan sahalewar ministan ma'aikatar, Adegboyega Oyetola a yau Laraba 25 ga watan Oktoba, Tribune ta tattaro.
Yaushe Tinubu ya yi sabbin nade-naden?
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai ta zamani, David Olusegun shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane gargadi Tinubu ya yi wa sabbin wadanda aka nadan?
Tinubu ya bukaci sabbin wadanda aka nadan da su yi aiki tukuru don ba da ta su gudunmawa kasar.
Wadanda aka nadan sun hada da manajan hukumar NIWA, Alhaji Munirudden Bola Iyebamiji da takwaransa na NSC, Mista Akutah Pius Ukeyima.
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Tinubu ya amince da nadin manyan mukamai guda biyu a hukumomi karkashin ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya.
"Nadin na zuwa ne bayan sahalewar ministan ma'aikatar, Adegboyega Oyetola.
"Wadanda aka nadan sun hada da babban daraktan hukumar NIWA, Alhaji Munirudden Bola da kuma na hukumar NSC, Mista Akutah Ukeyima."
Munirudden ya kammala digiri dinsa a fannin banki da kudade da kuma digiri na biyu a bangaren gudanarwa da harkokin kasuwanci.
Bola ya na da kwarewa a fannin tattalin arziki har na tsawon shekaru 28, ya kuma rike kwamishinan kudi a jihar Osun na tsawon shekaru takwas.
Yayin da Ukeyima ya kammala digiri dinsa na farko da na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.
Tinubu ya nada Ola Olukoyede sabon shugaban EFCC
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC.
Tinubu ya nada Ola ne wanda kwararren lauya da ya shafe shekaru ya na aiki a hukumar.
Hakan na zuwa ne bayan dakatar da tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa a farkon hawanshi karagar mulki.
Asali: Legit.ng