Jaruma Tonto Dikeh Ta Fice Daga Jam'iyyar ADC Zuwa APC Mai Mulki
- Jarumar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Tonto Dikeh, ta sauya sheƙa daga ADC zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Ta samu kyakkyawar tarba daga shugabar matan APC ta ƙasa, Mary Alile, da mataimakin sakataren watsalar a hedkwatar Abuja
- Jarumar ta yi takarar mataimakiyar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben gwamnan juhar Ribas amma ba su samu nasara ba
FCT Abuja - Fitacciyar jarumar shirya fina-finai a masana'antar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Tonto Dikeh, ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jam'iyyar APC ta ƙasa ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa tare da Hotuna shafinta na manhajar X wacce aka fi sani da Twitter a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, 2023.
A cewar sanarwan da jam'iyya mai mulki ta fitar, Jarumar ta tabbatar da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance ne ranar Litinin ɗin nan da muke ciki.
Shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Mary Alile tare da mataimakin sakataren watsa labaran jam'iyyar ta ƙasa, Duro Meseko, ne suka karɓi jarumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigan-jigan sun tarbi shahararriyar jarumar a hukumance a heskwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Yadda ta shiga siyasa tsundum a 2023
Dikeh ta kasance daya daga cikin manyan 'yan wasan kwaikwayo da jaruman fim da suka tsoma hannu dumu-dumu a siyasa yayin da ake dab da babban zabe na 2023.
Jarumar ita ce 'yar takarar mataimakin gwamna karkashin inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen gwamnan jihar Ribas da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.
A zaɓen bana, an ga jaruman Fim daga arewa da kudancin Najeriya sun shiga siyasa ka'in da na'in, wasu sun tsaya takara a jam'iyyu daban-daban.
Nuhu Abdullahi, fitaccen jarumin Kannywood na ɗaya daga cikin waɗan da suka tallata jam'iyyar APC musamman a matakin zaben shugaban ƙasa.
Kotun Koli Ta Kori Karar da Sanata Adeyemi Ya Shigar da Ododo
A wani rahoton kun ji cewa Kotun ƙoli ta kori karar da Sanatan Adeyemi ya kalubalanci nasarar Ahmed Ododo a zaben fidda gwanin APC a jihar Kogi.
A zaman yanke hukunci ranar Litinin, Kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancanta, ta kuma ci tarar mai ƙara.
Asali: Legit.ng