Kotun Koli Ta Dage Sauraron Daukaka Karar Atiku, Peter Obi
- Kotun ƙoli ta yanke hukuncin ɗage sauraron ƙararrakin da ke kalubalantar nasarar Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa
- Kotun ƙoli a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, ta yi fatali da karar da APM ta shigar na neman soke zaben Tinubu kan cewa bai cancanta ba
- Sai dai, lauyoyin APC, INEC, da Tinubu ba su ki amincewa da hukuncin da kotun ta yanke na ɗage sauraron ƙarar ba
FCT, Abuja - Kotun kolin Najeriya ta ɗage sauraron ƙararrakin da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da takwaransa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen da aka gudanar na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ku tuna cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta bayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma Atiku da Obi sun ƙi amincewa da sakamakon inda suka garzaya kotu.
Mutanen biyu sun ƙalubalanci sakamakon zaben tare da ɗan takarar jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) amma kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi fatali da ƙarar da suka shigar.
Ɓangarorin uku sun shigar da ƙara a kotun ƙolin wacce ta saurara a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar APM
Sai dai, Chukwuma Umeh, lauyan APM, ya nemi janye ƙarar bayan kotun ƙoli ta ƙi amincewa da buƙatar ta na soke zaɓen Tinubu.
Jam'iyyar ta yi iƙirarin cewa ba a maye gurbin Ibrahim Masari, wanda shugaban ƙasa ya zaɓa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na riƙo, a cikin kwanaki 14 da sashe na 33 na dokar zaɓe ya kayyaɗe ba, amma kotun ƙoli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar, cewar rahoton The Punch.
Sai dai, kotun ta cigaba da sauraron ƙararrakin jam'iyyuun PDP da LP.
Kotu ta ɗage ɗaukaka ƙarar Atiku, Peter Obi
Kotun mai alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro ta ɗage cigaba da shari’ar bayan muhawarar lauyoyin ɓangarorin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wannan ɗaukaka ƙarar an tanada hukunci har zuwa ranar da za a sanar da bangarorin," A cewar Okoro.
Kotun Koli Ta Magantu Kan Wasikun CSU
A wani labarin kuma, kotun ƙoli ta yi magana kan wasiƙun da jami'ar jihar Chicago ta bayar dangane da shaidar karatun Shugaba Tinubu.
Kotun ta bayyana cewa wasiƙun guda biyu sun ci karo da juna, sannan ta rasa ta wacce za ta yi aiki da ita a cikinsu.
Asali: Legit.ng