Cikakken Jerin Kararrakin Zaben da Kotun Daukaka Kara Ta Saurara a Kwana 9 da Suka Wuce

Cikakken Jerin Kararrakin Zaben da Kotun Daukaka Kara Ta Saurara a Kwana 9 da Suka Wuce

FCT, Abuja - Kotun daukaka ƙara a Najeriya (CoA) ta saurari wasu ƙararrakin zaɓe da aka yi a makon nan.

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da shugabar kotun daukaka ƙara, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta umurci jam'iyyun siyasa da lauyoyinsu da su mayar da duk wasu ƙararrakin da suka taso daga ƙararrakin zaɓe a faɗin ƙasar zuwa kotunan ɗaukaka ƙara na Abuja da Legas.

Kararrakin da kotun daukaka kara ta saurara
Akwai kararrakin zabe da dama a kotuna Hoto: Jibreel Muhammad Babangoshi, Senator Ishaku Abbo - SIA, Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Legit.ng ta gabatar da jerin ƙararrakin da suka shafi zabe da aka sauraresu a kotun ɗaukaka ƙara daga ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba zuwa Juma'a 20 ga watan Oktoba.

1) Shari'ar Natasha Akpoti

A ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba, kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci a ƙarar da aka shigar gabanta na ƙalubalantar hukuncin da kotun zaɓe ta yanke a zaɓen mazabar Kogi ta tsakiya na ayyana Natasha Akpoti a matsayin wacce ta lashe zaben.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku: Tsohon Jigon Jam'iyyar APC Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Alkalan Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpoti, mai shekara 43, ta yi takara ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

2) Kotun daukaka ƙara ta kori Sanatan Adamawa, Abbo

A ranar Litinin,16 ga watan Oktoba ne kotun ɗaukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun jihar Adamawa, ta yanke na ayyana Sanata Ishaku Elisha Abbo a matsayin Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa.

Sanata Abbo dai jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki.

Kotun ta umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga Rabaran Amos Yohanna a matsayin zaɓaɓɓen sanata.

3) Makomar Sanata Kingibe ta LP ba ta tabbata ba

Sai kuma a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta ɗage ƙarar da Philip Aduda (PDP) ya shigar gabanta yana ƙalubalantar nasarar Sanata Ireti Kingibe (Labour Party, LP).

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba Kan Yan Ta'adda, Sun Tura Masu Yawa zuwa Barzahu

Kotun wacce mai shari'a Daniel Kalio ya jagoranta bayan ya saurari bahasi daga bakin lauyoyin, ya ɗage cigaba da shari'ar zuwa ranar Laraba 18 ga watan Oktoba, 2023.

4) Kotun daukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar Otti

A ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, kotun ɗaukaka ƙara a Kano ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Abia, Alex Otti.

A hukuncin da ta yanke, kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke.

Idan dai ba a manta ba, hukuncin da mai shari’a M. N. Yunusa ya yanke a ranar 18 ga watan Mayu ya kori gwamnan Abia.

5) Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaben ɗan majalisar jihar Borno

Kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba, ta tabbatar da zaɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Askira-Uba/Hawul na jihar Borno, Midala Balami.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci Kan Tsige Gwamnan Da Ya Ci Zaɓe a 2023

Kotun ɗaukaka ƙara, a wani mataki na bai ɗaya da alkalai uku na kotun suka yanke, ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta.

Tsohon Jigon APC Ya Aike da Sako Ga Alkalai

A wani labarin kuma, tsohon jigon jam'iyyar APC, Timi Frank ya buƙaci alƙalan kotim ƙoli da su yi gaskiya wajen yanke hukuncinsu.

Kiran na Timi Frank na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ƙoli ke shirin fara sauraron ƙararrakin da aka ɗaukaka kan nasarar Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng