Timi Frank Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Alkalan Kotun Koli

Timi Frank Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Alkalan Kotun Koli

  • An isar da saƙo mai muhimmanci ga alƙalan kotun ƙoli guda bakwai da ke da alhakin yin la'akari da karar da ƴan takarar shugaban ƙasa uku suka gabatar a kan Shugaba BTinubu
  • Wannan sakon ya fito ne daga kwamared Timi Frank, tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC na ƙasa
  • Ya yi kira ga shugabannin alkalan da su ba da fifiko ga buƙatun Najeriya da al'ummarta maimakon son faranta ran wani daban

FCT, Abuja - An buƙaci alƙalan da ke jagorantar shari'ar kotun ƙoli a tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da su kalli ƙasar nan wajen gudanar da shari'ar.

Kwamared Timi Frank, tsohon mataimakin kakakin jam'yyar APC ne ya yi wannan roƙo a wata sanarwa da ya rabawa Legit.ng a Abuja a ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Bukaci Kotun Koli Ta Amince Ya Gabatar da Sabbin Hujjoji a Kan Tinubu, Ya Bayar da Kwararan Dalilai

Timi Frank ya aike da sako ga alkalan kotun koli
Timi Frank ya bukaci alkalan kotun koli su yi gaskiya Hoto: Timi Frank
Asali: Facebook

Alƙalan kotun ƙolin da za su saurari ƙararrakin sun hada da mai shari'a Musa Dattijo Muhammad, Uwani Musa Abba Aji, Lawal Garba, Helen M. Ogunwumiju, I.N. Saulawa, Tijjani Abubakar da Emmanuel Agim.

Wane kira Timi Frank ya yi?

Da yake roƙon Alƙalan, Frank ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun san cewa za a matsa muku, Alƙalai, domin ku yi abin da bai dace ba. Za a yi alƙawura, kyaututtuka da abubuwan jan hankali."
"Wasu daga cikinku sun kusa yin ritaya. Wane suna kuke son yin ritaya da shi? Shin kuna son yin ritaya da dukiyar da ta zubar da jini, idan aka yi la’akari da adadin mutanen da aka zubar da jininsu a lokacin zabe ba tare da natsuwa a cikin lamuranku ba?"
"Mutumin da yake so ku yi zalunci, ku ƙara tsanantawa ƴan Najeriya zai iya saka muku a yau. Shin kuma Allah zai kuɓutar da ku? Menene kuke so a tuna da ku bayan yin ritaya?”

Kara karanta wannan

Yan Majalisar Dokokin Jihar APC Sun Dakatar da Tsige Mataimakin Gwamna, Sun Bayar da Dalili

"Ku ceto dimokradiyyar Najeriya", Frank ga alƙalai

Ya ƙara da cewa roƙon da yake yi ba wai domin Atiku, Obi, ko jam’iyyar APM ba ne, “amma game da tarihin da za ku bari a Najeriya."

Frank ya bayyana cewa kotun ƙoli ita ce layin ƙarshe na kare dimokuradiyya, kuma dole ne tsarin doka ya cika aikinsa, wanda shine lokacin yin hakan.

Ya kuma bukaci alkalai da kada su nemi kare muradun wata jam’iyya ko mutum daya a kan ƴan Nijeriya sama da miliyan 200 na gida da waje, wadanda a yanzu haka suke jiran gaskiya ta tabbata.

A kalamansa:

"Muna kira ga alƙalai da su kasance masu jajircewa kamar irin ta kotun ƙoli ta Kenya wanda a yau ya zama misali mai haske da kuma nuni a matsayin shari’a na gaskiya da rashin son zuciya a nahiyar Afirka."
"Ku kare dokokin mu, ba muna neman ku ku yi wani abu da ya saba wa doka a matsayinku na 'yan Najeriya ba, amma ku mutunta kundin tsarin mulki, wanda ya haramtawa ƴan takara bayar da takardun shaida na jabu ga INEC."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Kada Ta Karbi Sabbin Hujjojin Atiku, Ya Bayyana Dalilansa

Kotun Koli Ta Sanya Ranar Sauraron Karar Atiku, Tinubu

A wani labarin kuma, kotun ƙoli ta sanya ranar da za ta fara sauraron ƙarar da Atiku Abubakar ya ɗaukaka a gabanta kan nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kotun ƙolin ta sanya ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta fara sauraron ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP ya shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng