Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Tsige Gwamnan Abia Na LP

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Tsige Gwamnan Abia Na LP

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara a Kano kan hukuncin babbar kotun tarayya na tsige shi da yan takarar LP
  • Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncin ƙaramar Kotun, inda ta ce ta gaza haɗa kowane ɓangaren Kes ɗin yayin yanke hukunci
  • Wani mutumi mai suna, Ibrahim Haruna Ibrahim ne ya shigar da ƙara mai lamba, FHC/KN/CS/107/2023, ya roƙi Kotu ta tsige dukkan 'yan takarar LP a Abia

Jihar Kano - Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya sake samun nasara a Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Kano.

Wannan nasara na zuwa ne makonni biyu bayan Kotun sauraron ƙorafin zaben gwamna ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Dalilai 4 da Ka Iya Sanyawa APC Ta Sha Kashi a Jihar Kogi

Gwamnan jihar Abiya ya samu nasara a Kotu.
Kotun ɗaukaka kara ta soke hukuncin tsige gwamnan Abia na Labour Party Hoto: Alex Otti
Asali: Twitter

Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, 20 ga watan Oktoba, 2023, Kotun ɗaukaka ƙara ta yi fatali da hukuncin babbar Kotun tarayya mai zama a birnin Kano.

Idan baku manta a hukuncin da mai shari'a M. N Yunusa na babbar Kotun tarayya ya yanke ranar 18 ga watan Mayu, ya tsige Gwamna Otti na Abia, Daily Independent ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a yau Juma’a ne kotun daukaka kara ta nuna rashin jin dadi kan yadda kotun ta yi gaggawar sauraren karar tare da yanke hukunci kan kes din.

Ta yanke hukuncin cewa babbar kotun tarayya ta yanke hukunci ba tare da shigar da kowane ɓangare ba, wadanda su ne ainihin waɗan da ake tuhuma a shari'ar.

Mene yasa Kotun ɗaukaka kara ta soke hukuncin?

Daga nan ne kotun daukaka kara ta ci tarar mai shigar da ƙara Naira miliyan daya (N1,000,000).

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

Wani mai suna, Ibrahim Haruna Ibrahim, ne ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya mai lamba FHC/KN/CS/107/2023.

A ƙarar ya roƙi kotun ta tsige dukkanin ‘yan takarar da jam’iyyar Labour Party ta tsayar a babban zaben 2023.

Gwamna Otti ne kaɗai ɗan takarar jam’iyyar LP da ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Abia da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Jerin alkalan da zasu saurari ƙarar Atiku da Obi a Kotun Ƙoli

Kuna da labarin An tsaida Alkalan da za su yi hukuncin karshe a kan shari’ar zaben shugaban kasar Najeriya na 2023 a kotun koli.

Helen Moronkeji Ogunwumiju da Uwani Musa Abba Aji su ne mata daga cikin Alkalan da kotun ta zabo su yi hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262