Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Cikin Barazana

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Cikin Barazana

  • Agbo Major ya kira ‘yan jarida ya sanar da su cewa rayuwarsa ta na cikin barazana a sakamakon rikicin siyasa da su ke ciki
  • Shugaban ‘yan tawaren na jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ya ce wasu sun zo sakataryarsu, ana neman shi da bindiga
  • Dr. Major ya tsira ne da yake wadanda aka aiko ba su san shi ba, ya kuma nuna ana masa barazanar kisa har a dandalin WhatsApp

Abuja - Agbo Major wanda ya zama shugaban ‘yan taware a jam’iyyar NNPP, ya nuna rayuwarsa ta na cikin barazana a halin yanzu.

Daily Trust ta rahoto Dr. Agbo Major ya na cewa wasu su na kokarin ganin bayan rayuwarsa, ana masa barazana har a WhatsApp.

Tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP ta kasan ya rikida ya na jagorantar tsagin da ke yaki da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

Shugabannin NNPP
Kwankwasiyya da NNPP su na rikici Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ana rikici da manyan jam'iyyar NNPP

Hakan ya na zuwa ne bayan ruguza majalisa da Dr. Boniface Aniebonam yake jagoranta, wanda ake ganin su ne su ka kafa NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatarsu da ke unguwar Wuse Zone 4, a birnin Abuja, ya zargi wasu da neman kashe shi.

Su wanene za su kashe shugaban NNPP

Major bai ambaci sunan kowa ba, amma ya tabbatar da cewa take-take sun nuna akwa wadanda su ka yi yunkurin hallaka shi cikin ofis.

"Babban dalilin kiran ku a yau (jiya) shi ne in sanar da ku yunkurin kashe ni da aka yi a ofishin nan a ranar Litinin 16 ga Agusta 2023.
Na zo nan da kusan karfe 2:45 na rana, jim kadan bayan nan sai wasu mutane biyu su ka shigo, su ka yi watsi da shawarar tsarin aiki daga jami’an da ke kan tebur a ofishin gaba.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Tona Komai, Ya Fadi Ainihin Masu Hana a Gyara Lantarki a Najeriya

Su ka shigo dauke da makami su na neman su gana da ni. Abin da ba su sani ba shi ne da ni su ke magana a lokacin."

- Agbo Major

Yadda Agbo Major ya sha da kyar

Daily Post ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa abin ya kai har daura masa bindiga a kai baya ga sakonni da aka aiko masa ta WhatsApp.

Kamar yadda ya labari, wadannan mutane sun bukaci shi ya kai su wajen “Major Agbo” da sunan sun yi karatun horas da soji tare a Jaji.

Da yake ya na da ragowar kwana a gaba, sai ya fada masu cewa wanda su ke nema bai nan, daga ya ce su ka arce a wata Toyota Corolla.

Haduwar NNPP da LP

Kafin zaben 2023,aka rahoto kakakin jam’iyyar NNPP, Dr. Agbo Major ya na cewa su na zama da LP da nufin a hada-kai domin a karbi mulki.

A karshe dai haduwar Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi ba ta yiwu a zaben ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng