APC Ta Fallasa Babachir, Ta Tona Abin da Ya Sa Yake Jin Haushin Shugaba Tinubu
- Jam’iyyar APC ta samu lokaci ta yi raddi ga Babachir David Lawal wanda ya ce Peter Obi ya fi kowa samun kuri’u a zaben 2023
- Duk da Bola Tinubu aka ayyana a matsayin wanda ya lashe takarar shugaban kasa, tsohon SGF ya na ganin an tafka murdiya ne
- Kakakin APC na kasa, Felix Morka ya na zargin dauko Kashim Shettima da aka yi a APC ya sa Babachir ya goyi bayan Peter Obi
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta maidawa Babachir David Lawal a kan ikirarin da ya yi na nasarar Peter Obi a takarar shugaban kasa.
Punch ta ce APC ta kula Injiniya Babachir David Lawal, ta na cewa ya na surutu ne saboda bai huce takaicin rasa mataimakin shugaban kasa ba.
Bola Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a APC a zaben 2023, jam’iyyar ta ce hakan ne ya yi wa Babachir ciwo.
APC ta soki Babachir David Lawal
Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya fitar da jawabi a makon nan, a matsayin raddi ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Felix Morka ya ce ‘dan siyasar ya na bukatar a zaunar da shi domin kuwa tsoma baki a kan batun da yake kotu, babban laifi ne a doka.
Yanzu haka APC da Bola Tinubu su na shari’a da Atiku Abubakar (PDP) da Peter Obi (LP) a kan zaben shugaban kasa da INEC ta shirya a bana.
Kotun koli ba ta yanke hukunci ba, amma Babachir David ya yi mata riga malam-masallaci, ya na cewa Bola Tinubu ne ya zo na uku a zaben.
Jawabin Felix Morka a kan zaben 2023
“Ya kamata Babachir Lawal ya san cewa yin sharhin son kai a kan batun da yake gaban kotun koli, karshen rashin sanin abin da ya dace ne.
Sai dai yanzu shi ya na jin haushi kuma ya na kulle da burinsa na zama abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne.
Shakka babu ya na bukatar kwararru su zaunar da shi kuma ya cancanci duk mu tausaya masa.
A zahiri yake, ba zai taba farfadowa daga fushin yin watsi da shi da Bola Tinubu ya yi a kwandon sharar siyasa ba."
- Felix Morka
Morka ya zargi Obi da amfani da siyasar addini kuma ya kunyata, ya kuma ce ko a siyasar Adamawa, ba a san da zaman Babachir Lawal ba.
"Tinubu ya zo na 3" - Babachir
A makon nan ne rahoto ya zo cewa Babachir David Lawal wanda ya rike Sakataren gwamnatin Najeriya ya ce LP ta yi nasara a zaben 2023.
‘Dan siyasar ya yi ikirarin Peter Obi ya zo na daya, Atiku Abubakar na biyu sai Bola Tinubu na uku.
Asali: Legit.ng