Majalisar Dattawa Ta Tabbatar a Nadin Shugabannin Hukumomin EFCC, NSIPA

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar a Nadin Shugabannin Hukumomin EFCC, NSIPA

  • Majalisar Dattawa a yau ta tabbatar da sabbin mukamai uku da Shugaba Tinubu ya tura musu don tantancewa
  • Majalisar ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC da sakatarensa, Mohammed Hammajoda
  • Har ila yau, majalisar ta kuma tabbatar da Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar walwalar jama’a, NSIPA

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC da sakatarensa, Mohammad Hammajoda.

Majalisar ta kuma tabbatar da Halima Shehu a matsayin shugabar Hukumar walwalar da jin dadin jama’a, NSIPA.

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin shugabannin EFCC, NSIPA
Majalisar Dattawa Ta Kammala Tantance Shugaban Hukumar EFCC. Hoto: EFCC.
Asali: UGC

Yaushe Tinubu ya tura shugabannin EFCC, NSIPA majalisa?

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya tura sunayen wadanda ya nada mukamai daban-daban a gwamnatinsa, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yaki Da Rashawa: Ka Da Ka Yi Misali Da Ni, Akpabio Ya Fada Wa Shugaban EFCC

Wadanda aka tabbatar din sun sha tambayoyi daga mambobin majalisar wanda su ka shafi bangaren da su ka fi kwarewa.

Tinubu ya nada matashiya Halima Shehu a matsayin shugabar Hukumar Walwalar Jama'a da Jin Kai ta NSIPA.

Har ila yau, Tinubu ya tura sunayen sabbin nade-naden da ya yi zuwa majalisar don tantance su, inda ya tura shugaban EFCC, Ola Olukoyede da sakataren Hukumar, Mohammed Hammajoda.

Meye ya faru yayin tantance shugaban EFCC?

Yayin tantance shugaban hukumar EFCC, an samu 'yar hatsaniya da ta koma raha a dakin majalisar a yau Laraba 18 ga watan Oktoba a Abuja.

Yayin tantance shi, Olukayode ya ambaci sunan shugaban majalisar, Godswill Akpabio yayin da ya ke jawabi yadda zai yaki cin hanci.

Akpabio ya dakatar da shi inda ya gargade shi da ya cire sunansa a misalin da ya ke na yaki da cin hanci, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban EFCC da Wasu 2 da Tinubu Ya Naɗa, Bayanai Sun Fito

Daga bisani bayan mambobin majalisar sun bushe da dariya, Olukoyede ya ci gaba da jawabinsa ba tare da saka sunan kowa ba.

Tinubu ya nada Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta EFCC.

Olukoyede zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa bayan dakatar da shi a matsayin shugaban hukumar da Tinubu ya yi a farkon hawanshi mulki.

Ola Olukoyede ya kasance kwararren lauya wanda ke da sanin makamar aiki na hukumar na tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.