Sakataren Watsa Labarai Na PDP Ya Shiga Hannun DSS

Sakataren Watsa Labarai Na PDP Ya Shiga Hannun DSS

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Benue ta koka kan rashin sanin inda sakataren watsa labaranta, Bemgba Iortyom, ya ke bayan amsa gayyatar DSS
  • Adzuwa Ashongo, ciyaman din PDP na Benue ta Arewa (Zone A), ya ce yana cikin jiga-jigan jam'iyyar da suka raka Iortyom zuwa hedkwatar DSS na jihar
  • Ashongbo ya ce jami'in yan sandan na farin kaya sun tafi da Iortyom, kuma ba a dawo da shi ba yamma sannan aka umurci su tafi

Makurdi, Benue - Jam'iyyar PDP reshen jihar Benue ya shiga damuwa a yayin da aka rahoto cewa sakatarenta na watsa labarai, Bemgba Iortyom, yana hannun jami'an yan sandan farin kaya, DSS.

Onarabul Adzua Ashongo, ciyaman din PDP na Benue ta Arewa (Zone A), ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba a Makurdi, babban birnin jihar, TVC ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Matashiya Yar Shekaru 25 Daga Arewa Wani Mukami Mai Muhimmanci

An tsare sakataren PDP a ofishin DSS
DSS ta tsare sakataren PDP: Hoto: PDP Update
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda DSS ta gayyaci Kakakin PDP a Jihar Benue

A cewar ciyaman din PDP, an gayyaci sakataren watsa labaran ne kan abin da za a iya cewa hira da shugaban yan sandan farin kayan a jihar.

Ashongo, cikin wata sanarwa, ya ce ba a bayyana dalilin da yasa yan sandan farin kayan suka gayyaci jigon PDPn ba.

Ya bayyana cewa shi da wasu jiga-jigan PDP sun raka sakataren watsa labaran zuwa hedkwatan DSS don amsa gayyata.

Ya bada bahasi cewa wani jami'in DSS mai suna Danlami Imam, wanda ya ce shi ke kula da sashin siyasa na hukumar, ya tarbe su. Ya kuma ce daga bisani ya dawo ya ce su tafi kada a ga kamar an tsare Iortyom ne.

Bayani dangane da Kakakin PDP da ke hannun DSS a Benue

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Babbar Sakateriyar Jam'iyyar PDP Ta Jiha, Bayanai Sun Fito

A cewar Ashongo, Imam ya kira su minti 20 bayan isansu sakatariyar jam'iyya cewa shugaban DSS baya nan duk da cewa sun taho amsa kiransa.

Ya ce sun isa ofishin DSS karo na biyu a ranar Litinin kuma jami'ai biyu da suka yi ikirarin daga ofishin shugaban hukumar suke, suka taho suka tafi da kakakin na PDP.

A cewarsa, jami'an sun ki yarda su raka Iortyom zuwa ofishin shugaban hukumar, suna mai cewa shi kakakin na PDP kadai aka gayyata.

Wani sashi na jawabinsa na cewa:

"Kuma har zuwa 6.17 na yamma da aka ce mu bar harabar hukumar, ba a san inda Mr Bemgba Iortyom ya ke ba; kuma ba a fada mana ko tsare shi aka yi ba ko ba tsare shi aka yi ba."

DSS: Bamu Kama Alkalin Kotun Zaben Gwamnan Kano Ba

A bangare guda, Hukumar DSS ta karyata wani rahoto da ke cewa jami’anta sun kama daya daga cikin alkalan kotun zabe gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Da Gaske NWC Ya Kori Sakataren Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Daga Muƙaminsa? Gaskiya Ta Bayyana

DSS din ta yi watsi da rahoton kana ta karyata zargin cewa gwamnatin jihar Kano ta yi cewa an kama daya daga cikin alkalan da suka soke nasarar zaben Gwamna Yusuf a zaben ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164