Shugaban APC, Ganduje Na Ganawar Gaggawa da ’Yan Majalisa a Ondo Kan Tsige Mataimakin Gwamna
- Dakta Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC ta kasa na wata ganawar gaggawa da ‘yan majalisun jihar Ondo
- Ganduje na wannan ganawar ce don shawo kan matsalar siyasa a jihar da kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar
- Wannan na zuwa ne kwanaki takwas bayan Ganduje ya kafa kwamiti don shawo kan wannan matsalar da ta ki cit a ki cinyewa
Jihar Ondo – Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje yanzu haka ya na ganawa da fusatattun ‘yan majalisar jihar Ondo.
Ganawar ba ta rasa nasaba da kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Ayiedatiwa.
Wasu matakai Ganduje ya dauka akn matsalar?
Tawagar wacce ta iso sakatariyar APC ta kasa da misalin karfe 1:25 na rana ta samu rakiyar gungun jami’an tsaro, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne kwanaki takwas bayan Ganduje ya kafa kwamitin da zai shawo kan ruguntsumin siyasa a jihar.
An kafa kwamitin ne don kawo mafita kan matsalar kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar da kuma shawartar jam’iyyar yadda za ta shawo kan wannan matsala.
Su waye a kwamitin sulhun da Ganduje ya kafa?
Wannan na zuwa ne bayan majalisar jihar Ondo sun yi ikirarin tsige mataimakin gwamnan kan wasu zarge-zarge da ke kansa.
Sun kuma sha alwashin ci gaba da shirin har karshe kamar yadda doka ta tanadar na tsige mataimakin gwamnan, Vanguard ta tattaro.
Daga cikin jiga-jigan APC kuma mabobin kwamitin Aminu Masari akwai ministan albarkatun ruwa, Adegboyega Oyetola da dan siyasa Sanata Jack Tilley daga jihar Benue.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Almakura da tsohon gwamnan jihar Ebonyi Martin Elechi da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, Daily Post ta tattaro.
Majalisar Ondo da musanta cewa ta dakatar shirin tsige Lucky
A wani labarin, Majalisar jihar Ondo ta musanta cewa ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Ayiedatiwa.
Majalisar ta ce ta na nan kan bakanta kuma wannan labari ba shi da tushe bare makama inda ta ce za ta ci gaba da shirin tsige shi har karshe.
Mambobin majalisar su ka ce sai sun kai karshe kan zarge-zargen da ake yi kan mataimakin gwamnan.
Asali: Legit.ng