Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Zaben Sanata Orji Kalu
- Kotun daukaka kara ta jadada nasarar Sanata Orji Uzor Kalu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
- Kotun daukaka karar ta yi watsi da karar da Mao Ohuabunwa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Nnamdi Iro Orji na Jam'iyyar Labour suka shigar
- Kotun ta ce zaben na tsohon gwamnan na jihar Abia ya bi ka'idoji da tanade-tanaden Dokar Zabe
Jihar Legas - Kotun Daukaka Kara, reshen Jihar Legas, ta yanke hukuncinta na karshe kan zaben Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa.
A hukuncin da dukkan alkalan suka yi tarayya a kai, kotun daukaka karar ta tabbatar da nasarar Kalu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, rahoton The Nation.
Ofishin watsa labarai na Kalu ne ya bayyana hakan cikin wata ta sanarwa a ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce zaben tsohon gwamnan na jihar Abia bi ka'idoji da tanade-tanaden Dokar Zabe.
Kotun ta ce Mao Ohuabunwa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Nnamdi Iro Orji na Jam'iyyar Labour sun gaza gamsar da kotu da hujojji da ke tabbatar da zarginsu na cewa ba a yi zabe ba a wasu rumfuna.
Ohuabunwa da Iro sun yi zargin cewa ba a yi zabe ba a rumfunan zabe fiye da 120 yawancinsu a kananan hukumomin Ohafia da Arochukwu a yankin.
A cewar Leadership, kotun ta kuma yi watsi da kokarin soke takarar Kalu kan cewa wai an taba samunsa da laifi a Babban Kotun Tarayya bisa laifin damfara.
Alkalan sun ce babu kwararran dalilan da ke nuna an same Sanata Orji Kalu da laifi karkashin sashi na 66 na Kundin Mulkin Najeriya domin Kotun Koli ta soke hukuncin samunsa da laifi din.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng